Labarai
Gwamna Umar Namadi Ya Kara Karfafa Gwiwar Matasa Domin Ci Gaban Jihar Jigawa
Gwamna Umar Namadi ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na ci gaba da kaddamar da ayyuka masu ma’ana don ci gaban jihar Jigawa.

Ya bada wannan tabbacin ne a wani taron jin ra’ayoyin jama’a a karamar hukumar Babura.

Malam Umar Namadi ya tunatar da matasa bukatar ganin sun kasance masu tarbiya da girmama na gaba da su, domin samun kyakkyawar rayuwa a gaba.

Shi ma da yake nasa jawabin, sakataren gwamnatin jihar, Malam Bala Ibrahim ya ce gwamnati mai ci a jihar ta bullo da shirin wayar da kan jama’a domin biyan bukatun jama’a da kuma sanya su cikin harkokin mulki.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, a yayin taron, sama da magoya bayan jam’iyyun PDP, da NNPP da SDP dubu daya da dari biyu ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, bisa la’akari da nasarorin da gwamnatin mai ci ta yi a jihar.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
