Labarai
CAN A Jihar Niger Ta Yi Watsi Da Dokar Hisbah
Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya reshen Jihar Niger State ta yi watsi da dokar Hisbah da Majalisar Dokokin Jihar Niger ta amince da ita kwanan nan.
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa kudirin dokar Hisbah da Majalisar Dokokin Jihar ta gabatar na nuna wariya da nuna bambanci ga Kiristoci a jihar.
Shugaban CAN na jihar, Mai Girma Uba (Most Reverend) Bulus Dauwa Yohanna, ya bayyana matsayar ƙungiyar a cikin wata sanarwa da aka bai wa ’yan jarida a Minna. Ya nuna damuwa cewa kudirin Niger State Hisbah Directorates Bill, wanda ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Chanchaga, Mohammed Abubakar, ya gabatar, kudiri ne mai cike da cece-kuce wanda bai kamata Gwamnan jihar, Umar Bago, ya sanya wa hannu ya zama doka ba.
Wani ɓangare na sanarwar Shugaban ya ce:
“Gwamna Mohammed Umar Bago, mu dukkan Kiristoci a jihar nan muna jan hankalinka kan wani abu da zai iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummar da kake jagoranta, kuma muna roƙonka da kada ka sanya wa wannan kudiri hannu ya zama doka.”
Shugaban CAN, wanda kuma shi ne Bishop na Katolika na Diocese na Kontagora, ya tambaya da cewa: “Me ya sa dokar Hisbah a Jihar Niger? Mene ne manufarta? Wane amfani za ta kawo wa al’ummarmu ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa? Shin ’yan majalisar sun fahimci cewa Kiristoci ba za su kasance ƙarƙashin dokar Hisbah ba?”
Bishop Bulus Yohanna ya ba da shawarar cewa akwai rundunar ’yan sandan Nijeriya, Hukumar Tsaron Fararen Hula (NSCDC), kungiyoyin sa-kai (Vigilante) da sauran hukumomi da ƙungiyoyi da kundin tsarin mulki ya ba su ikon aiki. Ya kuma yi kira ga dukkan al’ummar Jihar Niger masu kishin ƙasa—ba tare da la’akari da addini, kabila ko ra’ayin siyasa ba—da su haɗa murya domin tabbatar da cewa kudirin bai zama doka ba.
PR Aliyu Lawal
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
