Kasuwanci
Kungiyar Musulmai Ta Bada Gudunmawar Rijiyar Burtsatse Ga Sakatariyar CAN
A kokarin da ake na samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinin Kirista da Musulmi a jihar Neja, kungiyar ilimin addinin Musulunci ta bayar da tallafin rijiyar burtsatse ga kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da bikin, Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Arzika Abubakar Rimau ya ce IET ta yanke shawarar bayar da tallafin rijiyoyin burtsatse ne domin ta taimaka wajen farfado da dadaddiyar dangantakarsu.
“Samar da rijiyar burtsatse ga CAN na daga cikin kudurinmu na karfafa hadin kan addinai a jihar Neja”.
Rimau ya ce wannan karimcin na nuna dawwamammiyar gadon marigayi Sheikh Ahmed Lemu, wanda ya jajirce wajen hadin gwiwa tsakanin addinai tare da kulla alaka ta kut-da-kut da Malaman addinin Kirista kamar marigayi Father O’Connell, babban mai bayar da gudunmawa wajen ci gaban ilimi a jihar.
Yayin da yake nuna godiya a madadin al’ummar Kirista, Shugaban kungiyar CAN reshen Jihar Neja, Rabaran Bulus Dauwa Yohanna, ya bayyana matakin na IET a matsayin wata alama ta hadin kai, wanda ke karfafa hadin gwiwa tsakanin mabiya addinai biyu domin samun ci gaban al’umma.
Shima da yake nasa jawabin, Daraktan Sashen Hulda da Jama’a, Alhaji Ibrahim Yahaya ya yabawa Victoria Ndagi, wata Kirista mai kishin kasa, bisa yadda ta ja hankalin kungiyar kan bukatun ruwa na sakatariyar CAN da ke Minna babban birnin jihar Neja.
A matsayin wani ɓangare na taron, IET ta ba da lambar yabo ga Victoria Ndagi saboda rawar da ta taka wajen inganta haɗin gwiwa tsakanin addinai da haɓaka ci gaban al’umma.
An bayyana ta a matsayin wata gada tsakanin addinai, tare da lura da cewa shawarar da ta bayar ya sa IET ta fadada ayyukan jin kai ga sauran al’ummomin Kirista, saboda lambar yabo da aka ba ta ta dace sosai.
ALIYU LAWAL/Minna
-
Ilimi6 days agoGwamnatin Tarayya Ta Yi Alkawarin Inganta Hanyoyi, Ruwa da Wutar Lantarki a Jami’ar FUD
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Amince Da Shirin Gaggawa Na Kwana 120 Domin Farfaɗo Da Ilimi
-
Labarai6 days agoTinubu: Sabbin Dokokin Haraji Za Su Kawo Wadata Yayinda Tsofaffi Suka Talauta ‘Yan Najeriya
-
Labarai7 days agoHezbollah Da Isra’ila Za Su Yi Ganawar Gaba Da Gaba A Karon Farko
-
Labarai3 days agoƘungiyar Ci gaban Al’ummar Saminaka Ta Bai Wa ‘Yan Sanda Injin Hilux Don Ƙarfafa Tsaro
-
Labarai7 days agoAn Yi wa Yara Sama da 66,000 Rigakafin Cutar Shan Inna a Tarauni
-
Kasuwanci7 days agoMajalisar Neja ta Amince da Dokar Hana Ayyukan Baban Bola a Unguwanni
-
Labarai6 days agoHarin Shanga: Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafawa Iyalan Jama’an Tsaro da Aka Kashe
