Connect with us

Ilimi

Ana Aikin Hadin Gwiwa Don Kawo Karshen Cutukan HIV/AIDS Da Tarin Fuka

Published

on

Domin karfafa tsarin kiwon lafiya ta hanyar sa ido a tsakanin al’umma, kungiyar bayar da shawarwari ta COVID-19 (C19RM) ta jihar Kano ta kai ziyarar bayar da shawarwari ga Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Jihar Kano (SACA).

 

Ziyarar dai an yi ta ne da nufin sabunta ayukkan hukumar game da ci gaba da ziyarar wuraren da kungiyar C19RM Advocacy, Treatment, and Monitoring (ATM) ke aiwatarwa a karkashin sashin al’umma ta ACOMIN.

 

Tawagar ta hada da Abdulhakim Daiyab (Jami’in shirye-shirye na jihar C19RM), Dakta Nura Haladu (Shugaban ACOMIN na Jiha), Alhaji Sunusi Hashim (Shugaban kungiyar TB ta jiha), da Hafsat Muhammad (wakiliyar NEPHWAN).

 

Tawagar ta samu tarbar Dr Imam Wada, Daraktan Rigakafi da Kulawa, wanda ya wakilci Darakta Janar na SACA, Dakta Usman Bashir.

 

A yayin ziyarar, tawagar ta bayyana cewa, C19RM ATM ya dade yana ba da himma don inganta yaki kan cutar kanjamau, tarin fuka a matakan cibiyoyin kiwon lafiya kafin a kai ga magance matsalolin da ba a warware ba ga hukumomin da abin ya shafa.

 

Sun bayyana sakamakon binciken da suka yi a kwanan nan, wanda ya bayyana kalubalen da ke buƙatar sa baki cikin gaggawa don inganta aikin ba da kulawa na kiwon lafiya da kuma martanin da ya shafi al’umma dangane da cutar kanjamau.

 

Tawagar ta bayyana cewa, bayan ziyarar wuraren aiki, suna ba da ra’ayi ga ƙungiyoyin jama’a na CBOs da ƙungiyoyin sa ido na al’umma CLMTs.

Da yake mayar da jawabi, Dr. Imam Wada ya amince da kimar shirin na C19RM kuma ya tabbatar da shirin SACA na magance matsalolin da aka taso.

 

Ya jaddada kudirin hukumar na yaki da cutar kanjamau tare da jaddada cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta kuduri aniyar tabbatar da samar da ingantaccen kiwon lafiya ga kowa da kowa.

 

Ya kuma yaba da gudunmawar da tawagar C19RM ke bayarwa a duk fadin kananan hukumomin jihar Kano tare da ba su tabbacin ci gaba da haɗin gwiwa don cimma burin lafiya.

 

KHADIJAH ALIYU/KANO

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara