Connect with us

Labarai

Gwamnan Zamfara Ya Jaddada Bukatar Ganin Alkalai Suna Yanke Shari’a Akan Lokaci

Published

on

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bukaci sabbin alkalai a jihar da su mayar da hankali wajen hanzarta yanke shari’a a kotuna.

Gwamna Lawal ya bayyana hakan ne a yayin da ya jagoranci rantsar da sabbin alkalai na kotun koli da Khadiman Kotun Daukaka Kara ta Shari’a a fadar gwamnatin jihar da ke Gusau.

Gwamnan ya bayyana cewa an nada alkalan ne bayan tantancewa da kuma amincewar Hukumar Shari’a ta Kasa (National Judicial Council).

Da fari, ina taya ku murna bisa wannan muhimmin matsayi da kuka samu. Wannan nadin naku na nuni da tabbaci da kuma kwarin gwiwa da fannin shari’a ke da shi a kanku.”

Ya bukaci alkalan da su tabbatar da wannan kwarin gwiwa da aka nuna gare su ta hanyar nuna cikakkiyar kwarewa, gaskiya, rikon amana da adalci a ayyukansu.

Na kuma yaba da namijin kokari da jajircewar babbar mai shari’a ta Jihar Zamfara kuma Shugabar Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Jihar, Mai Shari’a Kulu Aliyu OFR, da daukacin tawagarta, bisa yadda  Hukumar Shari’a ta Kasa zta  amince da dukkan wadanda aka mika sunayensu su kuma aka nada su.”

“Wannan lokaci ne mai matukar muhimmanci ga bangaren shari’a na jihar don goyon bayan kokarin wannan gwamnati wajen inganta rayuwar al’umma. Hadin kai tsakanin bangaren zartaswa da na shari’a yana da matukar muhimmanci wajen cimma nasarorin da ake bukata.”

Dr. Lawal ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bayar da goyon baya ta hanyar samar da dukkan hakkoki, alawus-alawus da kuma ingantaccen yanayin aiki domin bai wa alkalai damar yin aiki yadda ya kamata.

Mai Shari’a Kulu Aliyu, Babbar Alkalin Jihar Zamfara, ce ta jagoranci rantsar da sabbin alkalan uku na kotun koli da kuma khadiman kotun daukaka kara guda uku.

Sabbin alkalai na kotun koli da aka rantsar su ne: Garba Sirajo, Rabi Bashir da Abdullahi Nasir. Sai kuma
Khadiman da sun hada da: Ibrahim Jibril, Muhammad Sanusi Magami da Sha’aban Mansir.

 

Daga Aminu Dalhatu

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara