Labarai
Bauchi ta kafa kwamitin Limamai da Fastoci don tabbatar da zaman lafiya a Tafawa Balewa da Bogoro
Gwamnatin jihar Bauchi ta kaddamar da wani kwamiti na musamman na Limamai da Fastoci domin samar da hadin kai da zaman lafiya a kananan hukumomin Tafawa Balewa da Bogoro bayan wani rikici da ya barke a yanki kwanakin baya.
Gwamnan jihar Bala Muhammad a lokacin da yake kaddamar da kwamitin a gidan gwamnati da ke Bauchi ya ce bai zai yi kasa a qwiwa ba wajen daukan matakan da su ka da ce don magance barazanar bata gari da ke kokarin wargaza zaman lafiya da tsaro a yankunan.
Bala Muhammad ya ce zaman lafiya shine ginshikin kashin bayan kowace al’umma don haka akwai bukatar a hada malaman addini musamman Limamai da Fastoci don su suka fi kusa da Al’ummah da kuma dimbin mabiya domin wayar da kan mabiyansu kan zaman lafiya da kuma zimmar dakile sa ke barkewar rikici a kananan hukumomin biyu.
Gwamnan ya bukaci mambobin kwamitin da su yi aiki tare da masu ruwa da tsaki daban-daban don tabbatar da dorewar zaman lafiya da aka samu a kananan hukumomin biyu cikin shekaru da dama da suka gabata wanda a yanzu aka samu tsaiko sakamakon rikicin manoma da makiyaya da ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi.
Ya bukace su da su kai rahotonin duk wani abu da su ke zargi da ya wuce ikon su ga hukumomin tsaro da abin ya shafa domin daukar matakin gaggawa.
“Ba za mu bari wani ya lalata zaman lafiyar da muka gina ba,” in ji Gwamnan. “Wannan kwamitin zai zama gada tsakanin al’umma, domin samar da fahimtar juna da zaman lafiya.”
Gwamnan ya yi bayanin ayyukan kwamitin da su ka hada da wayar da kan jama’a kan samar da zaman lafiya da tattaunawa da yin sulhu a tsakanin jama’a da nufin haka ta cimma ruwa.
Da suke mayar da martani a madadin kwamatin, Shuwagabanin kwamitin Faizu Ado Musa daga karamar hukumar Tafawa Balewa da Reverend Father Benson Bature daga karamar hukumar Bogoro sun yi alkawarin yin aiki tukuru har sai an dawo da zaman lafiya mai dorewa a yankunan.
“Za mu yi duk mai yiwa wajen sake nauyin da aka dora mana da taimakon Allah. Kuma in Allah yarda duk wadda ya ke da hannu wajen tayar da rikici a yankunanmu Allah ba zai bar shi ba”.
Shugabannin hukumomin tsaro daban-daban da suka hada da kwamishinan ‘yan sandan jihar, daraktan tsaro na jiha. Kwamandojin soji na sama da kasa da sauransu na daga cikin waya’nda su ka halarci taron.
Cov/Alhassan.
-
Labarai4 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai5 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai1 day agoHukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani
-
Labarai5 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai2 days agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai4 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
-
Labarai4 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
