Labarai
Baragurbi a Aikin Jarida na Barazana ga Sahihancin Kafafen Yada Labarai – Shugaban NUJ-FRCN
Shugaban Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen FRCN Kaduna, Kwamared Umar Adamu Sarkinfada, ya bayyana cewa mummunan aikin jarida na zama babbar barazana ga ƙwarewa da amincewar jama’a da kuma zaman lafiyar ƙasa.
A cikin sakon sabuwar shekara da ya aikewa ’yan jarida, Sarkinfada ya gargaɗi cewa yaɗa labaran ƙarya da rashin kwaklwaran binciken jarida da kuma ayyukan mutanen da ba su da horo amma suke kiran kansu ’yan jarida, na lalata martabar aikin jarida tare da raunana ayyukan sahihan ’yan jarida.
Ya bayyana cewa rahotannin da ba a tantance ba kuma masu tayar da hankali, musamman kan muhimman batutuwan ƙasa, na iya haddasa firgici, yaɗa bayanan ƙarya da kuma tashin hankalin al’umma, yayin da ayyukan marasa ƙwarewa ke bata sunan ’yan jarida masu bin ka’ida.
Shugaban NUJ ya yi kira ga ’yan jarida da su sake tsayawa tsayin daka kan ɗabi’un aikin jarida, yana jaddada muhimmancin sahihanci, daidaito, tantance gaskiya da yin cikakken bincike bisa manufofin NUJ da ƙa’idar aiki.
Ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su ƙarfafa hanyoyin sa-ido na cikin gida tare da bada horo na ci gaba mai muhimmanci, yayin da ya shawarci jama’a da su yi dogara ga sahihan hanyoyin labarai tare da tantance bayanai kafin su yaɗa su.
Sarkinfada ya sake jaddada kudurin reshen NUJ FRCN Kaduna na inganta ƙwarewa da mutuncin kafafen yaɗa labarai, yana bayyana sabuwar shekarar a matsayin wata dama ta sabunta jajircewa ga aikin jarida mai inganci a Najeriya.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai22 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
