Labarai
Ƙaruwa a Shan Abubuwan Sha Masu Ƙara Ƙarfi na Haddasa Damuwar Lafiya a Kano
Abubuwan sha masu ƙara ƙarfi, waɗanda aka fi sani da energy drinks ko energizers, na ƙara samun karɓuwa a faɗin Nijeriya, inda Jihar Kano ke fuskantar gagarumar ƙaruwa a yawan masu shansu.
A ‘yan lokutan nan, kamfanoni da dama sun shiga harkar samar da abubuwan sha masu ƙara ƙarfi sakamakon ƙaruwa da buƙatarsu a ƙasar nan.
Matasa, manya, har ma da mata na shan waɗannan abubuwan sha da yawa, ba tare da la’akari da sana’a ko salon rayuwarsu ba, kuma galibi ba sa yin tunanin illolin da hakan ka iya haifarwa ga lafiyarsu.
Duk da shahararsu a tsakanin al’umma, ƙwararrun masana lafiya na gargaɗin cewa yawan shan abubuwan sha masu ƙara ƙarfi na iya haifar da manyan matsalolin lafiya.
A Kano, ana samun waɗannan kayayyaki cikin sauƙi a shaguna, manyan kantuna da kuma kan manyan hanyoyi, inda ‘yan talla da masu shago ke samun yawan ciniki a kullum.
Shirin Grassroots Nigeria ta tattauna da wasu mazauna Kano, inda da dama daga cikinsu suka ce suna shan abubuwan sha masu ƙara ƙarfi ne domin ƙara kuzari, hana barci na dogon lokaci, ko kuma ƙarfafa jiki yayin aiki da harkokin yau da kullum.
Da yake magana kan illolin lafiyar da ke tattare da shan abubuwan sha masu ƙara ƙarfi, wani ƙwararren likita a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Dr. Musa Muhammad Bello, ya gargaɗi jama’a da su guji yawan shansu.
Dr. Bello ya bayyana cewa shan waɗannan abubuwan sha da yawa na iya haifar da munanan cututtuka. A cewarsa, yawan shansu na iya janyo hawan jini, lalacewar hanta, cututtukan ƙoda, da sauran matsalolin lafiya.
Ya shawarci jama’a da su rage yawan shan abubuwan sha masu ƙara ƙarfi, tare da neman madadin hanyoyi masu lafiya wajen ƙara kuzari.
Masana lafiya na ci gaba da kira da a ƙara wayar da kan jama’a game da haɗarin shan abubuwan sha masu ƙara ƙarfi ba tare da tsari ba, musamman a tsakanin matasa.
Khadijah Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
