Connect with us

Labarai

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta Shiga Jimami Sakamakon Rasuwar ‘Yan Majalisar 2 a Awa Guda

Published

on

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta shiga jimami mai tsanani sakamakon rasuwar ’yan majalisar su biyu Honarabul Sarki Aliyu Daneji da Honarabul Aminu Sa’adu Ungogo, waɗanda suka rasu a ranar Laraba, da tazarar awa ɗaya kacal.

An ruwaito cewa Honarabul Daneji, wanda ke wakiltar Mazabar Kano Municipal a Majalisar Dokokin Jihar Kano, ya rasu ne kimanin awa ɗaya bayan rasuwar abokin aikinsa, Honarabul Aminu Sa’adu Ungogo.

Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, Sanusi Dawakin Tofa ne ya tabbatar da rasuwar Daneji cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Tun da farko dai, Majalisar ta yi babban rashi na Aminu Sa’adu Ungogo, ɗan majalisar da ke wakiltar Mazabar Ƙaramar Hukumar Ungogo kuma Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar.

Ungogo, mamba ne na jam’iyyar NNPP kuma rahotanni sun nuna cewa ya rasu ne bayan gajeriyar jinya.

Majiyoyi daga cikin Majalisar sun bayyana cewa marigayi  Ungogo ya halarci Majalisar Dokokin Jihar Kano a ranar da ya rasu, inda ya shiga taron kwamitinsa, lamarin da ya ƙara girgiza abokan aikinsa da ma’aikatan Majalisar.

Rasuwar ’yan majalisar biyu a kusan lokaci guda ta jefa Majalisar cikin alhini tare da girgiza harkokin siyasa a faɗin Jihar Kano.

’Yan majalisa, shugabannin jam’iyyu, jami’an gwamnati da al’ummar mazabunsu na ci gaba da bayyana alhini da kaɗuwa kan wannan lamari, suna bayyana rasuwar a matsayin babban koma baya ga ayyukan Majalisar Dokokin jihar.

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara