Labarai
Gwamna Namadi Ya Rattaba Hannu Kan Kasafin Shekarar 2026
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya rattaba hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2026 na Naira biliyan 901 da miliyan 804, domin inganta ci gaban jihar tare da biyan buƙatun al’ummar Jigawa.
Da yake jawabi bayan sanya hannu kan kasafin, Gwamna Namadi ya bayyana cewa duk da kasafin jihar ya kai sama da Naira Biliyan, kasafin kuɗin haɗin gwiwa na ƙananan hukumomi 27 ya kai Naira Biliyan 288 da Miliyan 805.
“Wannan kasafi sakamakon shirin tattaunawa da al’umma ne da muka gudanar, kuma yana nuna ainihin muradu da burin mutanen Jihar Jigawa.

“Saboda haka, kasafin al’umma ne, daidai yadda jama’a suka buƙata, kuma daidai abin da ke ƙunshe a cikin wannan kasafi,” in ji gwamnan.
Gwamnan ya kuma yabawa mambobin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa bisa jajircewa da sadaukarwar da suka nuna a duk tsawon aikin kasafin kuɗin.

“Goyon bayansu a yayin tarukan tattaunawa da al’umma, ganawar bangarori biyu, tattaunawa ta manyan shugabanni, da kuma matakan kwamitoci, ya taka muhimmiyar rawa wajen amincewa da wannan kasafi cikin nasara,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma yabawa mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar bisa amincewa da kuma shiga shirin tattaunawa da al’umma, tare tattara ra’ayoyin jama’a, inda da dama daga cikinsu ke aiki har cikin dare.

Haka nan, Namadi ya yaba wa al’ummar jihar bisa goyon baya da kuma halartar su a tsarin kasafin kuɗin, inda ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta yi iya ƙoƙarinta wajen inganta rayuwar al’ummar Jigawa.
-
Ilimi7 days agoFarfesa Gumel Ya Fitar da Sabon Tsari da Zai Daga Martabar FUD
-
Labarai3 days agoHukumar Raya Kogin Benuwe Ta Bullo da Sabuwar Fasahar Kare Hanyar Ban-ruwa a Tafkin Geriyo
-
Ilimi3 days agoAn Gudanar da Liyafar Taya Murna ga Sabon Shugaban Jami’ar Tarayya Dutse
-
Labarai5 days agoGwamnatin Tarayya ta Bada Tallafin Kayayyakin Aiki Gona ga Ƙananan Manoma a Jigawa
-
Labarai6 days agoAn Fara Bikin Kamun Kifi da Al’adu na Ƙasa da Ƙasa na Argungu na Bana
-
Labarai4 days agoGwamnatin Jigawa ta Amince da Shirin Ciyarwar Watan Ramadan na Bana
-
Labarai6 days agoHukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Ja Hankalin Maniyyata Game da Muhimmancin Halartar Taron Bita
-
Labarai6 days agoJigawa: Hukumar Alhazai ta Bai wa Amirul Hajji Tabbacin Cikakken Goyon Baya
