Labarai
Najeriya Ta Shirya Karɓar Wasannin Kungiyar Kasashen Renon Ingila A 2030– Tinubu
Najeriya ta tabbatar da shirinta na karɓar Wasannin Kungiyar Kasashen Renon Ingila na 2030, inda za ta zama ƙasar Afirka ta farko da za ta kafa wannan tarihi tun 1930.
Shugaba Bola Tinubu, ta bakin Shugaban Ma’aikatansa Femi Gbajabiamila, ya ce gwamnati ta ba da cikakken goyon baya, ta kuma shirya samar da dukkan abubuwan more rayuwa, tsaro da masauki kafin lokaci.
A jawabansu daban daban, Shugaban Hukumar Wasanni ta Kasa Shehu Dikko da Shugaban Kungiyar Wasannin Renon Ingila Habu Gumel, sun bayyana cewa Najeriya ce damar Afirka mafi cancanta, yayin da kwamitin neman karɓar gasar ya gabatar da shirin gudanar da wasanni 15, ciki har da kwallon ƙafa.
Najeriya da Indiya ne ke neman karɓar gasar, inda za a bayyana kasar da za a yi wasannin a watan Nuwamba 2025.
Bello Wakili
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
