Labarai
Matasa 8 Sun Sami Tallafin Kasuwanci Na Miliyan 2 A Jigawa
Matasa takwas a jihar Jigawa sun lashe tallafin kasuwanci na Naira miliyan biyu daga British Council ƙarƙashin shirin Youth Connect.
Kowane ɗaya daga cikinsu ya samu Naira dubu dari biyu da hamsin domin fara ayyukan kasuwanci.

An gudanar da shirin ne tare da haɗin gwiwar Kings Trust International, CITAD, da gwamnatin jihar Jigawa.
Matasa tamanin aka horas a tsawon makonni takwas kan kasuwanci, fasahar zamani da kuma ƙwarewar tallatawa, inda daga cikinsu guda takwas suka fito a matsayin zakaru.

Wakilin British Council, Dr. Yahaya Janga, ya shawarci matasan da su yi amfani da horon da suka samu da kuma tallafin wajen kafa kasuwanci mai dorewa. Ya kuma yaba wa gwamnatin Jigawa da sauran abokan hulɗa da suka tallafa wa shirin.
Shi ma Daraktan CITAD, Farfesa Yunusa Zakari Ya’u, ya ce shirin na nufin bai wa matasa ƙwarewar da zata taimaka musu wajen samun ayyukan yi da kuma dogaro da kai.

A nasa jawabin, Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jigawa, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya ce gwamnatin jihar na baiwa ci gaban matasa muhimmanci, tare da jan hankalin waɗanda suka ci gajiyar da su yi amfani da tallafin yadda ya dace.
Waɗanda suka ci nasarar, sun gode wa British Council, Kings Trust International da CITAD bisa wannan damar da suka samu.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
