Labarai
Jihar Nasarawa Ta Tara Harajin Sama Da Naira Biliyan 16 A Wata 8
Hukumar Haraji ta Nasarawa ta Hukumar Tara Haraji ta Jihar Nasarawa ta tara Naira biliyan 16 da Miliyan 500 daga watan Janairu zuwa Agustan 2025.
Shugaban Hukumar, Alhaji Ahmed Yakubu Mohammed, ne ya bayyana hakan lokacin da ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa kan Kuɗi da Kasafin Kuɗi, a wajen tantance rahoton aiwatar da kasafin kuɗi na zango na biyu na shekarar 2025 a Lafia.
Alhaji Ahmed Yakubu ya bayyana cewa hukumar ta samu nasara sosai, inda ya danganta nasarorin da suke samu ga goyon bayan da Gwamna Abdullahi Sule da kuma Majalisar Dokokin Jihar ke ba su.
Ya bayyana cewa kuɗaɗen da aka tara sun fito ne daga harkar ma’adinai, bankuna da kamfanonin gine-gine da sauran hanyoyi.
Shugaban hukumar ya tabbatar da cewa za su ci gaba da himma wajen nemo ƙarin hanyoyin da za su taimaka domin ƙara samun kuɗaɗe ga baitul-malin jihar.
Tun da farko, shugaban kwamitin, Alhaji Hudu A. Hudu, ya bayyana cewa an gudanar da binciken ne domin tantance yadda hukumar ta aiwatar da kasafin kuɗi na zango na biyu na shekarar 2025.
Ya yaba wa hukumar bisa ƙoƙarin da ta yi na ƙara kudaden shiga ga baitul-mali na jihar.
Alhaji Hudu ya shawarci hukumar da ta ƙara himma wajen samar da ƙarin kuɗaɗe ga gwamnati.
Shugaban kwamitin ya yaba wa hukumar bisa nasarorin da suka cimma ya zuwa yanzu, tare da tabbatar musu da ƙarin haɗin kai da goyon bayan da zai taimaka musu su samu nasarori masu yawa nan gaba.
Daga Aliyu Muraki
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
