Labarai
Karamar Hukumar Gwarzo Ta Raba Magunguna Da Kayan Aiki Ga Asibitoci
A yunƙurinta na inganta harkar kiwon lafiya, Karamar Hukumar Gwarzo ta raba muhimman magunguna da kayan aikin ga cibiyoyin kiwon lafiya a gundumomi 10.
An gudanar da bikin mika kayan a Cibiyar Musulunci ta Gwarzo, inda Shugaban Karamar Hukumar Dakta Mani Tsoho Abdullahi, wanda ya sami wakilcin mataimakinsa Alhaji Abdulmumin Garba Lakwaya, ya jagoranci taron.
Kayayyakin da aka raba sun haɗa da na’urar auna hawan jini, na gwajin siga, da wasu kayan aiki daban-daban da aka tanada domin ƙarfafa aikin cibiyoyin lafiya tare da faɗaɗa damar jama’a na samun ingantacciyar kulawa.

Yayin da yake jawabi, Lakwaya ya jaddada bukatar ma’aikata su jajirce wajen aiki da gaskiya da rikon amana. Ya tunatar da su cewa an samar da kayayyakin ne domin amfanin marasa lafiya kai tsaye, daidai da kudirin karamar hukumar wajen samar da ingantaccien kiwon lafiya.
Mataimakin Shugaban ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da kuma Dakta Gwarzo bisa ci gaba da ƙoƙarin inganta rayuwar jama’a.
Shi ma Kansilan Lafiya na Karamar Hukumar, Alhaji Nazifi Gambo Salihawa, ya jawo hankalin cibiyoyin lafiya kan bin ƙa’idojin rahoton lafiya na Najeriya, inda ya bukace su da su tabbatar da bin ka’ida wajen rubuta da kuma amfani da sabbin kayayyakin domin samun inganci, da kuma amincewar al’umma.

Wasu daga cikin shugabannin cibiyoyin da suka karɓi kayayyakin sun tabbatar da cewa za a raba magungunan bisa adalci tare da amfani da su yadda ya dace domin biyan bukatun lafiya na jama’a.
Taron ya samu halartar Kakakin Majalisar Karamar Hukumar, kansiloli, shugabannin cibiyoyin lafiya, da sauran masu ruwa da tsaki.
Daga Khadijah Aliyu
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
