Labarai
Tinubu Ya Yi Ta’aziyya Ga Gwamnatin Kebbi Bisa Rasuwar Sarkin Zuru
Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi ta’aziyya ga gwamnatin Jihar Kebbi da al’ummar jihar bisa rasuwar Sarkin Zuru, Mai Martaba, Manjo Janar Muhammadu Sani Sami (Gomo II).
A cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana rasuwar Sarkin a matsayin “babban rashi ga ƙasa,” inda ya tuno irin hidimar da marigayin ya yi a matsayinsa na tsohon gwamnan soja na Jihar Bauchi da kuma hidimarsa a matsayin basarake.
Shugaba Tinubu ya lura cewa Najeriya za ta daɗe tana tuna gudummawar tsohon janar ɗin, wanda kuma ya yi yaƙi a matsayin ƙaramin hafsan soja lokacin Yaƙin Basasa.
Shugaban ƙasa ya kuma yabawa jagorancin marigayin, wanda ya ce ya kawo zaman lafiya da cigaba a masarautar Zuru da Jihar Kebbi baki ɗaya.
Ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya jikan sarkin da rahama, ya kuma ba iyalansa da jama’arsa haƙurin jure wannan babban rashi.
Daga Bello Wakili
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
