Connect with us

Labarai

An Yi Jana’izar Muhammadu Buhari A Gidansa Da Ke Daura

Published

on

An bizne gawar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a gidansa da ke garin Daura.

Babban limamin Daura, Sheikh Hassan Yusuf ne ya jagoranci Sallar janazar a filin da ke kusa da gidan marigayin.

Bayan kammala sallar jana’izar, babban limamin Daura tare da Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, sun gabatar da addu’o’in neman rahama ga tsohon shugaban ƙasar.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da Firaministan Nijar Ali Lamine Zaine, da Shugaban Ƙasar Guinea-Bissau Umaru Sissoco, da tsohon Shugaban Ƙasar Nijar Muhammadou Issoufou, da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo sun halarci jana’izar.

Jakadu daga ƙasashe, sanatoci da ’yan majalisun jihohi da na tarayya, gwamnoni, ministoci, manyan ’yan kasuwa da shugabannin masana’antu daga sassa daban-daban na ƙasa sun halarci jana’izar domin girmama tsohon shugaban ƙasan.

Wakilanmu sun ruwaito cewa gagarumin cunkoson jama’a ya toshe dukkan hanyoyi masu shiga da fita daga Daura, musamman hanyar Mai’adua, inda gidan marigayin ya ke.

Tun da farko, Shugaba Tinubu tare da Shugaban Guinea Bissau da Firaministan Nijar sun karɓi gawar marigayi Muhammadu Buhari a filin jirgin sama na Umaru Musa Yaradua da ke Katsina, jim kaɗan bayan zuwanta daga Landan.

Shugaba Tinubu ya jagoranci faretin soja  tare da hafsoshin soja na ƙasa, suka ɗauki gawar zuwa motar da aka tanadar don kai ta Daura. Sannan Shugaba Tinubu da baƙinsa suka raka gawar a cikin dogo jerin gwanon motoci.

Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya shugabanci Najeriya a matsayin soja da farar hula, ya rasu yana da shekaru tamanin da biyu (82) a duniya.

 

Daga Isma’il Adamu

Labarai

Labarai7 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara