Ilimi
Dalibai Sama Da 200 Sun Sami Digiri Mai Daraja Ta Daya A FUD
Jami’ar Tarayya ta Dutse (FUD) ta ce dalibai 209 za su karbi shaidar digiri mai daraja ta daya a taron yaye dalibai karo na 8 da na 9 da aka shirya gudanarwa a wannan wata.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da ‘yan jarida kan shirye-shiryen da aka kammala domin taron yaye daliban a Dutse, Jihar Jigawa.
Ya ce, kididdigar yawan daliban da za a yaye ta nuna cewa, jimillar dalibai 1,271 sun samu digiri mai daraja ta biyu matakin farko(SecondClassUpper), yayin da dalibai 2,034 suka samu digiri mai daraja ta biyu, mataki na biyu, kasa (Second Class Lower), sannan kusan dalibai 559 suka samu digiri mai daraja ta uku (Third Class).
Ya bayyana cewa, adadin jimillar daliban da za a yaye ya kai 4,277.
Farfesa Abdulkarim ya kara da cewa, adadin daliban da ke karatu a jami’ar ya karu daga 202 a shekarar 2011/2012 zuwa 18,000 a halin yanzu, tare da karuwar kwasa-kwasai daga guda 5 a 2011/2012 zuwa guda 45 a yau.
Shugaban Jami’ar ya bayyana cewa, za a gudanar da laccar taron yaye dalibai karo na 8 da 9, inda tsohon Shugaban Jami’ar na farko, Farfesa Jibrilla Dahiru Amin, zai gabatar da makala.
Ya ce taken laccar shi ne: “Amfani da Bincike da Kirkire-kirkire Domin Cimma Ci gaba mai Dorewa a Najeriya: Rawar da Manyan Makarantu Ke Takawa.”
Haka zalika, ya bayyana cewa, an kammala ginin sashen ilimin shari’a na jami’ar, inda za a fara karbar dalibai a wannan sashe daga zangon karatu na gaba.
Ya ce, shirin kafa Sashen Kimiyyar Magunguna (Pharmaceutical Sciences) na daga cikin abubuwan da ake kan tsarawa a halin yanzu.
Farfesa Abdulkarim ya bayyana cewa, cikin shekaru hudu da suka gabata, jami’ar ta samu tallafin bincike fiye da Naira miliyan 800, ciki har da Naira miliyan 113 da kamfanin Google ya bayar domin kafa dakin binciken Artificial Intelligence(binciken kwakwaf ta yanar gizo), wanda shi ne na farko a cikin manyan makarantu a yankin Arewa maso Yamma.
Haka kuma, Farfesa Abdulkarim ya bayyana cewa, kwanan nan jami’ar ta rattaba hannu kan yarjejeniya da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da Hukumar Samar da Wutar Lantarki ga Yankunan Karkara domin gina rukunin hasken rana na zamani mai karfin megawatt 1.6 wanda zai tabbatar da cewa harabar jami’ar za ta rika amfani da wutar lantarki ta hasken rana.
Ya kuma jaddada cewa daga cikin ayyukan da aka kammala a jami’ar akwai sabon ginin Majalisar makarantar(Senate Building), ginin sashen koyar da ilimin shari’a (Faculty of Law), sabon dakin karatu(Library) , dakunan daukar darasi gudabiya masu cin daliba 250 kowannensu, da dakunan koyar da Kimiyya da Fasaha (STEM), da dakunan kwana guda biyu na mata da sauran su.
Farfesa Mohammed ya nuna godiyarsa ga ‘yan jarida a fadin jihar Jigawa da wajen jihar bisa hadin kai da goyon baya da suke baiwa jami’ar.
Daga karshe, ya yaba wa ma’aikatan jami’ar bisa hadin kai da jajircewarsu, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen cimma nasarorin da Jami’ar ta samu.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai5 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai7 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai18 hours agoHukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani
-
Labarai2 days agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
