Kasuwanci
Sanata Abdulaziz Yari Ya Bada Tallafin Taki Sama Da Naira Biliyan 1.3 Ga Manoman Zamfara.
Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta yamma, Alhaji Abdulaziz Yari Abubakar, ya biya sama da naira biliyan 1.3 a matsayin tallafin taki ga manoma a fadin jihar a wani bangare na tallafawa noma na shekarar 2025.
Shugaban Kwamitin Rarraba Taki, Dokta Lawal M. Liman ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar duba Kamfanin taki na ASAD, wani kamfanin hada takin zamani da ke karamar hukumar Bungudu a Jihar Zamfara.
Dokta Liman ya tabbatar da cewa, tuni kamfanin ya tanadi tireloli 81 na takin da aka ba da odar takin zamani domin rabawa.
A wata sanarwa da shugaban kwamitin yada labarai na jihar, Ibrahim Muhammad ya fitar, kuma ya rabawa manema labarai a Gusau, ya bayyana cewa, manyan masu cin gajiyar tallafin kananan manoma ne, wadanda su ne kashin bayan harkokin noma na jihar.
“Manufar farko ita ce tallafa wa kananan manoma don kara yawan amfanin gona da samun kudin shiga ta hanyar samun taki mai sauki a lokacin damina,” in ji Dokta Liman.
Dokta Liman, wanda kuma yake rike da mukamin Shugaban Hukumar Gudanarwa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH), Shika, Zariya, Jihar Kaduna, ya bayyana cewa, a karkashin tsarin bayar da tallafin, kowane mai cin gajiyar shirin zai biya Naira 20,000 kan buhun taki, idan aka kwatanta da farashin kasuwa na Naira 45,000 zuwa 50,000 a halin yanzu.
Ya kara da cewa za a kai takin ne kyauta zuwa kowace hedikwatar karamar hukuma domin tabbatar da samun sauki ga manoma a fadin jihar.
Ya ba da tabbacin cewa rabon da za a fara nan bada jimawa ba, ba za a yi siyasa ko bangaranci ba.
REL/AMINU DALHATU.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
