Connect with us

Ilimi

Dalibai Sama Da 200 Sun Sami Digiri Mai Daraja Ta Daya A FUD

Published

on

Jami’ar Tarayya ta Dutse (FUD) ta ce dalibai 209 za su karbi shaidar digiri mai daraja ta daya a taron yaye dalibai karo na 8 da na 9 da aka shirya gudanarwa a wannan wata.

Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da ‘yan jarida kan shirye-shiryen da aka kammala domin taron yaye daliban a Dutse, Jihar Jigawa.

Ya ce, kididdigar yawan daliban da za a yaye ta nuna cewa, jimillar dalibai 1,271 sun samu digiri mai daraja ta biyu matakin farko(SecondClassUpper), yayin da dalibai 2,034 suka samu digiri mai daraja ta biyu,  mataki na biyu, kasa (Second Class Lower), sannan kusan dalibai 559 suka samu digiri mai daraja ta uku (Third Class).

Ya bayyana cewa, adadin jimillar daliban da za a yaye ya kai 4,277.

Farfesa Abdulkarim ya kara da cewa, adadin daliban da ke karatu a jami’ar ya karu daga 202 a shekarar 2011/2012 zuwa 18,000 a halin yanzu, tare da karuwar kwasa-kwasai daga guda 5 a 2011/2012 zuwa guda 45 a yau.

Shugaban Jami’ar ya bayyana cewa, za a gudanar da laccar taron yaye dalibai karo na 8 da 9, inda tsohon Shugaban Jami’ar na farko, Farfesa Jibrilla Dahiru Amin, zai gabatar da makala.

Ya ce taken laccar shi ne: “Amfani da Bincike da Kirkire-kirkire Domin Cimma Ci gaba mai Dorewa a Najeriya: Rawar da Manyan Makarantu Ke Takawa.”

Haka zalika, ya bayyana cewa, an kammala ginin sashen ilimin shari’a na jami’ar,  inda za a fara karbar dalibai a wannan sashe daga zangon karatu na gaba.

Ya ce, shirin kafa Sashen Kimiyyar Magunguna (Pharmaceutical Sciences) na daga cikin abubuwan da ake kan tsarawa a halin yanzu.

Farfesa Abdulkarim ya bayyana cewa, cikin shekaru hudu da suka gabata, jami’ar ta samu tallafin bincike fiye da Naira miliyan 800, ciki har da Naira miliyan 113 da kamfanin Google ya bayar domin kafa dakin binciken Artificial Intelligence(binciken kwakwaf ta yanar gizo), wanda shi ne na farko a cikin manyan makarantu a yankin Arewa maso Yamma.

Haka kuma, Farfesa Abdulkarim ya bayyana cewa, kwanan nan jami’ar  ta rattaba hannu kan yarjejeniya da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da Hukumar Samar da Wutar Lantarki ga Yankunan Karkara domin gina rukunin hasken rana na zamani mai karfin megawatt 1.6 wanda zai tabbatar da cewa harabar jami’ar za ta rika amfani da wutar lantarki ta hasken rana.

Ya kuma jaddada cewa daga cikin ayyukan da aka kammala a jami’ar akwai sabon ginin Majalisar makarantar(Senate Building), ginin sashen koyar da ilimin shari’a  (Faculty of Law), sabon dakin karatu(Library) , dakunan daukar darasi gudabiya masu cin daliba 250 kowannensu, da dakunan koyar da Kimiyya da Fasaha (STEM), da dakunan kwana guda biyu na mata da sauran su.

Farfesa Mohammed ya nuna godiyarsa ga ‘yan jarida a fadin jihar Jigawa da wajen jihar bisa hadin kai da goyon baya da suke baiwa jami’ar.

Daga karshe, ya yaba wa ma’aikatan jami’ar bisa hadin kai da jajircewarsu, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen cimma nasarorin da Jami’ar ta samu.

Usman Muhammad Zaria

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara