Connect with us

Labarai

Mutane Sama Da 207 Ne Suka Rasu Sakamakon Ambaliyar Ruwa A Mokwa

Published

on

Mutane sama da dari biyu da bakwai (207) ne suka rasu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afkawa al’ummar karamar hukumar Mokwa a jihar Neja.

 

Shugaban Hukumar Kula da Yanayi da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Abdullahi Baba Arah, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Minna, game da kokarin da hukumar ke yi wajen rage radadin bala’o’i da dama da suka hada da fashewar tankokin mai a Agaie da Diko, hare-haren ‘yan bindiga da kuma ambaliya mai muni da ta auku kwanan nan a Mokwa, domin hana faruwar hakan nan gaba.

 

A cewarsa, mutane sama da 500 ne suka jikkata sakamakon ambaliyar, yayin da ba a tantance adadin wadanda suka bace ba tukuna. Ya ce, ko a jiya Talata, 2 ga watan Yuli na wannan shekara, wasu jami’an hukumar za su tashi daga Minna zuwa Mokwa domin ci gaba da aikin taimakon gaggawa da tattara bayanai.

 

Da yake magana kan wadanda gidajensu ko kadarorinsu suka lalace, ya bayyana cewa an baiwa kowane mutum Naira 500,000 domin samun damar haya a wuri mai kyau, tare da wasu tallafin kayan abinci da aka raba ga dukkan wadanda bala’in ya shafa don rage musu radadi.

 

Abdullahi Baba Arah, ya kara da cewa an  samu nasarar wannan kokari ne bisa goyon baya da gaggauta daukar mataki da Gwamnan jihar , Mohammed Umar Bago ya yi, wanda ya bayyana a matsayin jajirtaccen gwamna.

 

Shugaban hukumar ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa tare da nuna godiya ga dukkan wadanda suka bada gudunmawa domin rage radadin bala’in da ya auku, tare da yin kira da a ci gaba da bayar da taimako domin cimma nasara.

 

Abdullahi Baba Arah ya kuma yi amfani da damar wajen yi kira al’ummar jihar Neja da ke zaune a yankunan bakin kogi, musamman wadanda ke kan hanyoyin ruwa, da su gaggauta barin wuraren  domin kaucewa hadurran da ke tattare da ambaliya.

 

Daga Aliyu Lawal

 

 

Labarai

Labarai21 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai23 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara