Labarai
Jirgin Karshe Na Alhazan Jihar Kwara Ya Isa Kasa Mai Tsarki
Sahun ƙarshe na mahajjata 140 daga jihar Kwara, ciki har da jami’an NAHCON, da ya tashi daga filin jirgin sama na Babatunde Idiagbon da ke Ilori ya isa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025.
Yayin jawabi ga mahajjatan kafin tashin su da misalin ƙarfe 6:42 na yammacin Laraba, Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai na Jihar Kwara, Farfesa Mashood Mahmud-Jimba, ya shawarci mahajjatan da su kasance masu ɗabi’a a lokacin da suke kasa mai tsarki.

Farfesa Mahmud-Jimba ya bayyana cewa an shirya duk abin da ya dace domin tabbatar da cewa mahajjatan sun gudanar da aikin hajji ba tare da wata matsala ba.
Ya kuma shawarce su da kada su yi ayyuka masu wahala domin samun damar shiryawa yadda ya kamata don gudanar da ibadarsu.
Shugaban ya kuma ja hankalinsu da su yi amfani da cibiyoyin lafiya da aka samar idan suna buƙatar magani.
A nasa jawabin, Amirul Hajj na Jihar Kwara na shekarar 2025, kuma Olupo na Ajase-Ipo, Barista Ismail Yahaya-Alebiosu, ya bayyana jin daɗinsa da irin shirin da aka yi domin jigilar mahajjatan zuwa Saudiyya.
Ya yaba wa gwamnan jihar bisa bayar da goyon baya da kayayyakin aiki ga hukumar domin tabbatar da gudanar da aikin hajji ba tare da tangarda ba.
Barista Yahaya-Alebiosu ya kuma shawarci mahajjatan da su kiyaye dokoki da ƙa’idodi yayin da suke kasa mai tsarki.
A nasa bangaren, Sakataren zartarwa na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kwara, Alhaji Abdulsalam Abdulkadir, ya shawarci mahajjatan da su zama jakadun ƙasa nagari.
Ya kuma bukace su da su yi addu’a domin zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin ƙasa yayin da suke a kasa mai tsarki.
Jimillar mahajjata 2,210 daga jihar Kwara ne ake sa ran za su gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
