Labarai
Rukunin Karshe Na Alhazan Jigawa Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki
Rukunin ƙarshe na mahajjatan Jigawa 368 ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Nuhu Muhammadu Sunusi zuwa Saudiyya don aikin hajjin shekarar 2025.
A wata hira da aka yi da shi a Radio Nigeria kafin tashinsu gaf da Asubahin Alhamis, Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana cewa rukunin ƙarshe na mahajjatan 368 sun fito ne daga ƙananan hukumomin Birnin Kudu, Buji, da Taura na jihar.

A cewarsa, wannan rukunin ƙarshe ya haɗa da Amirul Hajj na jihar, malamai masu wa’azi, wasu jami’an shiyyoyi da cibiyoyi, da kuma wasu jami’an hukumar.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana cewa, jihar ta kammala aikin tantance mahajjata cikin nasara ba tare da wata tangarda ba.

Ya yabawa Gwamnan jihar, Malam Umar Namadi, bisa goyon baya da haɗin kai da ya bayar ga hukumar.
Darakta Janar ɗin ya kuma yi kira ga sauran mahajjatan Najeriya da ba a ɗauka ba su ƙara haƙuri tare da ci gaba da karanta littattafan da aka basu lokacin bita da shirye-shiryen hajji a jiharsu.


A jawabin bankwana da ya gabatar a filin jirgin sama, Gwamna Umar Namadi ya shawarci mahajjatan da su yi addu’a don jiharsu da ƙasar baki ɗaya.
Namadi ya kuma ja hankalinsu da su bi dokokin da ƙasar Saudiyya ta shimfiɗa.


Wasu daga cikin mahajjatan da suka yi magana da Radio Nigeria kafin tafiyarsu sun gode wa Allah da ya basu damar zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin bana.
Sun yabawa shugabannin hukumar kula da jin daɗin mahajjata ta jihar Jigawa bisa tanadin abinci da abin sha da suka yi musu yayin da suke sansanin Alhazai da filin jirgi.


Mahajjatan sun bayyana jin daɗinsu da yadda aka tsara wa’azi tare da yabawa jami’an hukumar da yadda suka kula da su a sansanin Alhazai.
Radio Nigeria ya ruwaito cewa, jami’an hukumar shige da fice, kwastam, da NDLEA ne suka tantance mahajjatan tare da jakunkunansu masu nauyin kilo 8.
Usman Muhammad Zaria.
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai5 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai5 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai3 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai3 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
