Connect with us

Labarai

Hajjin 2025: Jihar Kaduna Ta Yi Tanadin Masauki Na Musamman Ga Alhazan Bana

Published

on

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta samu nasarar samo ingantaccen masauki  ga alhazan jihar a birnin Makkah, gabanin gudanar da aikin Hajjin 2025.

Daya daga cikin mambobin kwamitin musamman da ke kula da aikin hukumar, Malam Buhari Marabar-Jos ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata a Kaduna.

Buhari Marabar-Jos ya bayyana cewa masaukan sun cika dukkan sharuddan da Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da Ma’aikatar Hajji ta Saudiyya suka gindaya.

Ya kuma bayyana cewa wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar, tana can ƙasar Saudiyya don kammala sauran shirye-shirye kafin dawowarsu Najeriya.

Ya jaddada cewa Gwamna Uba Sani ya  ƙuduri aniyar kula da jin daɗin alhazan jihar, tare da tabbatar da cewa gwamnati ta himmatu matuƙa wajen ganin an gudanar da aikin Hajji cikin sauƙi da nasara.

Ya yi kira ga maniyyata aikin Hajjin bana da su ci gaba da halartar taron bita na mako-mako da hukumar ke gudanarwa a faɗin ƙananan hukumomi 23 na jihar.

 

Safiyah Abdulkadir

 

Labarai

Labarai13 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai2 days ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai2 days ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara