Labarai
‘Yan Sanda Sun Fara Bincike Kan Kisan Shugaban Kungiyar Miyetti Allah A Kwara
Rundunar ‘Yan sanda a jihar Kwara ta ce ta fara bincike kan kisan da aka yi wa Alhaji Idris Abubakar, shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na jihar.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi ya fitar, ya ce an harbe shugaban ne a ranar 8 ga Maris, 2025 a kofar gidansa da ke Oke-Ose, a unguwar Ilorin.
A cewar sanarwar Jami’an ‘yan sanda sun garzaya inda lamarin ya faru nan take, inda suka gano kwamson harsashi guda biyar da aka yi amfani da su wajen yin harbin.
Ya bayyana cewa Hukumar Binciken Laifukan Jiha (SCID) ta fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Ta kuma bada tabbacin za a gano, tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kuliya, sannan ta bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da bayar da bayanai masu muhimmanci ga ‘yan sanda.
A halin da ake ciki kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Kwara, ta bayyana kaduwarta dangane da kisan da aka yi wa shugaban ta Alhaji Idris Abubakar Sakaina, wanda wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kashe a gidansa da ke Oke-ose da misalin karfe 10 na dare.
A wata sanarwa da shugaban Fulanin (Ardon Ardodi) a jihar Kwara, Alhaji Ojonla Mahmud ya fitar dauke da sa hannun sakataren kungiyar MACBAN ta jihar, AbdulAzeez Muhammed ya bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta zakulo wadanda suka gudu domin tabbatar da sun fuskanci hukunci.
Sanarwar ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta taimaka wa iyalan mamacin wajen samar da ingantaccen ilimi ga yaran da kuma kyautata jin dadinsu.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
