Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Kano Ta Bullo Da Sabbin Hanyoyin Kare Makarantunta Daga Kalubalen Tsaro

Published

on

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ce gwamnatinsa ta dauki wani muhimmin mataki na tabbatar da tsaron makarantunta, inda za a hada hannu da masu ruwa da tsaki  don kara karfafa tsaro a yankunan da makarantu suke.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin bikin bude taron masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro a jihar  da kuma horas da jami’an tsaron makarantu, wanda aka gudanar a fadar gwamnatin jihar.

 

Gwamnan wanda kwamishinan Ilimi Alhaji Ali Haruna Makoda ya wakilta, ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki  kudirin gwamnatinsa na bunkasa fannin ilimi a jihar.

Ya ce yayin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar kalubale wajen tabbatar da tsaro a makarantu, wannan shirin wani muhimmin mataki ne na karfafa tsaro da inganta yanayin koyo.

A jawabinsa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abayomi Shogunle, ya jaddada muhimmancin tsaro a makarantun, inda ya bayyana cewa abu ne da  gwamnati mai ci ta ba da fifikoa kai.

Ya yi nuni da cewa, Sifeto janarna ‘yan sanda ne ya kaddamar da rundunar tsaro ta makarantu da nufin magance matsalolin tsaro a makarantun firamare da sakandare da manyan makarantu.

Shi ma a nasa jawabin mataimakin shugaban jami’ar Aliko Dangote, Farfesa Musa Tukur Yakasai, ya yabawa horon kan  inganta tsaro a cibiyoyin ilimi.

Tun da farko Sufeto Janar na ‘yan sanda Kayode Egbetokun, wanda mataimakin sufeto janar shiyya ta daya AIG Ahmad Ammani ya wakilta, ya jaddada muhimmancin hada hannu tsakanin jama’a da jami’an tsaro domin magance matsalar rashin tsaro a makarantu da cibiyoyi.

Taron mai taken “Karfafa Tsaro da Hadin Kan Al’umma wajen Kare Ilimi,” ya hada wakilai daga ‘Yan sandan Najeriya, da rundunar Soji, da cibiyoyin ilimi da dai sauransu.

Taron ya samu halartar shugabannin hukumomin tsaro na Kano da sauran masu ruwa da tsaki.

Abdullahi Jalaluddeen

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara