Connect with us

Ilimi

UNICEF Zai Shawo Matsalar Yawan Yara Da Ba Sa Zuwa Makaranta A Arewa Maso Yammacin Najeriya

Published

on

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar.

Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025.

Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare,  da kuma miliyan daya  da dubu dari daya da saba’in da shidd, da dari tara da goma sha takwas(1,176,918), a matakin kananan makarantun sakandare, wanda ya bayyana a matsayin abin ban tsoro.

Ya gano wasu kalubalen da ke ci gaba da faruwa a halin da ake ciki  baya ga makaranta, da suka hada da rashin isassun kudade, da rashin kula da al’adu, da rashin isassun kayayyakin more rayuwa a makarantu, da karancin ma’aikata da gudun hijira sakamakon ambaliyar ruwa da sauran illolin sauyin yanayi.

Yayin da Arewa maso Yammacin Najeriya ta kasance ta biyu a kasar da ba a zuwa makaranta, lamarin da ake fama da shi a jihohin Kano da Jigawa da Katsina yana da ban tsoro.

Abin da ya kara ta’azzara shi ne sakamakon rashin ingantaccen ilimi ga yaran da suka yi sa’ar shiga makaranta.

A halin yanzu akwai kimanin yara miliyan goma da dari biyu a matakin firamare da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, inda kashi 16 cikin 100 sun fito ne daga jihohin Kano, da Jigawa da Katsina, a cewar rahoton MICS  na shekarar 2021.

Kusan yara miliyan daya ne ba sa zuwa makaranta a jihar Kano da jimillar mutane 989,234, yayin da a Jigawa ana da jimillar 337,861 sai  jihar Katsina da ke da yara 536,112 da ba sa zuwa makaranta.”

Mr Farah ya bukaci gwamnatocin jihohin Kano, da Jigawa da Katsina da su daidaita kasafin  kudi tare da fitar da su a zahiri ga bangaren ilimi daidai da abin da ake bukata na Manufofin Ci Gaba Mai Dorewa na SDG da ma’aunin Hukumar kula da Ilimi, da Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) don ingantacciyar sakamako a fannin.

Ya kuma yi kira ga gwamnatocin wadannan jahohin da su tunkari kalubalen samun ilimi ta hanyar fadada abubuwan more rayuwa a makarantu da daukar kwararrun malamai da shigar da makarantun kur’ani a cikin tsari na yau da kullun.

 

Daga Isma’il Adamu

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara