Labarai
An Gudanar Da Taron WASA Na Rundunar Sojin Najeriya A Gusau
Kwamandan runduna ta 1 ta sojojin Najeriya da ke Gusau, Birgediya Janar Opurum Timothy, ya bayyana wa al’ummar jihar Zamfara da ma kasa baki daya aniyar rundunar sojojin Najeriya na ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron wasannin rundunar sojojin Najeriya ta yammacin Afirka WASA 2024 da aka gudanar a Gusau.
Taro West African Social Activities WASA wani taro ne na shekara-shekara da rundunar sojojin Najeriya ke shiryawa domin wasannin gargajiya na wannan yankin na Afirka.

Taron na shekara-shekara yana tattaro Jami’ai, Sojoji, da iyalansu cikin annashuwa domin wasannin al’adun da kuma bikin ƙarshen shekara.

Janar Opurum wanda ya jaddada kudirin rundunar na kawar da ‘yan fashi da kuma dawo da zaman lafiya a Zamfara da yankin Arewa maso Yamma gaba daya, ya yi kira ga sojojin da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu, yana mai jaddada cewa, sadaukarwarsu da na da matukar muhimmanci wajen samun zaman lafiya mai dorewa.

Kwamandan Birgediya wanda ake yi wa lakabi da “Jar Kunama”, ya yabawa al’ummar Zamfara bisa yadda suke ba da hadin kai, musamman ta hanyar samar da muhimman bayanan sirri, wanda ya haifar da gagarumar nasara.

Tun da farko, Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara, wanda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Meriga ya wakilta, ya yabawa rundunar sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro bisa namijin kokarin da suke yi na samar da zaman lafiya mai dorewa a fadin jihar ta Zamfara.
Taron WASA na bana a Gusau ya samu halartar manyan baki da suka hada da sarakunan gargajiya da shugabannin sauran hukumomin tsaro kamar rundunar sojojin saman Najeriya da jami’an tsaro da dai sauransu.

Muhimman abubuwan da suka faru a wajen taron sun hada da, baje kolin al’adu da raye-raye, wasan kokowa, da dai sauransu.
Yayin da wasu da dama da suka yi nasara suka je gida da kyaututtuka daban-daban da suka hada da man girki, shinkafa da sauran kyaututtuka.
Daga Aminu Dalhatu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
