Ilimi
NIEPA Ta Jinjinawa UNICEF Bisa Kare Hakkokin Yara Na Samun Ilimi A Najeriya
Cibiyar Tsare-tsaren Harkokin Ilimi da Gudanarwa ta Kasa (NIEPA) ta yaba da kokarin Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) wajen kare hakkokin yara na samun ilimi a Najeriya.
Darakta Janar na Cibiyar, Dakta David Shofoyeke ne ya bayyana hakan yayin bude taron horaswa na kwanaki uku ga masu gudanar da shirye-shiryen ilimin yankuna (LESOP) a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.
Dakta Shofoyeke, wanda Dakta Grace Omiyale Babbar Malamar Horaswa da Bincike a Cibiyar ta wakilta, ya tabbatar da cewa cibiyar tana da cikakken kudiri na sauya tsarin ilimi a Najeriya.

Ya bayyana cewa, samar da cikakken tsarin ilimi na jiha da kuma tsarin aiwatar da shirye-shiryen ilimi na jihohi yana taimakawa jihohi wajen tsara burinsu a fannin ilimi.
Ya ce, ta wannan hanya ce jihohi za su iya aiwatar da shirye-shiryen ilimi da suka dace da manufofi da albarkatun da ake da su.
Dakta David ya kara da cewa UNICEF tana bayar da taimakon fasaha wajen shirya wadannan takardu a jihohi takwas.
A cewar NIEPA, UNICEF ta shimfida tubalin shirye-shiryen ilimi bisa hujja, masu daidaito tsakanin jinsi, da fama da nakasassu, tare da karfin jurewa rikice-rikice da sauyin yanayi a Najeriya.
Dakta David ya yaba wa Gwamnatin Jihar Jigawa bisa jajircewarta wajen sauya tsarin ilimi ta hanyar amfani da bayanai wajen yanke shawara.

Shi ma babban sakatare na ma’aikatar ilimin gaba da sakandare, da fasaha da kimiyya ta jihar, Alhaji Muhammad Dahiru, ya yaba wa abokan hulɗa bisa shawarwarin da suke bayarwa.
A cewarsa, Gwamnatin Jihar Jigawa tana da cikakken kudiri na yin aiki tare da abokan hulda domin samar da ingancin ilimi a jihar.
Dahiru ya ce daya daga cikin ginshikan gwamnatin Namadi shi ne sauya tsarin ilimi.
Hukumar UNICEF tare da hadin gwiwar Tarayyar Turai (EU), suna tallafa wa Jihar Jigawa wajen nazarin sabon tsarin dabarun ilimin jihar.
Wannan aikin yana gudana ne karkashin shirin hadin gwiwa na UNICEF da EU kan ilimi da karfafa matasa.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
