Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Jigawa Ta Jinjinawa UNICEF Da EU Bisa Gudunmawarsu A Fannin Ilimi

Published

on

Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba wa Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da Tarayyar Turai (EU) bisa gudunmawar su wajen inganta harkar ilimi a fadin jihar.

Shugaban Hukumar Ilimin Firamare (SUBEB) na jihar, Farfesa Haruna Musa, ne ya bayyana hakan a lokacin bude taron bitar kwana uku na karkashin Shirin Ayyukan Sashen Ilimi na a Jihar, wato Local Education Sector Operations Plan (LESOP) da aka gudanar a Dutse.

Ya bayyana cewa UNICEF da Tarayyar Turai na tallafa wa gwamnatin jihar ta hanyar Shirin Inganta Ilimi da Karfafa Matasa  da Shirin Ayyukan Sashen Ilimi na jihar Jigawa inda ake sake dubawa da tsara sabbin tsare-tsaren aiki da za su zama jagora wajen inganta harkar ilimi a jihar.

A cewarsa, wannan shiri zai mai da hankali kan magance matsalolin da suka addabi tsarin ilimi, musamman matsalar karancin sakamako mai kyau a fannin koyo da kuma yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta.

A nasa jawabin, Manajan Ilimi na ofishin UNICEF na Kano, Mista Michael Banda, ya sake jaddada kudirin UNICEF din na ci gaba da hada kai da gwamnatin Jigawa wajen farfado da fannin ilimin firamare. Ya ce bitar LESOP muhimmin mataki ne wajen karfafa tsarin shiryawa da aiwatar da manufofin ilimi a jihar.

Mista Banda ya ce sake duba LESOP na nuna cewa gwamnatin jihar tana da niyyar bin sahihin tsarin yanke shawara bisa hujja, gaskiya da kuma hada al’umma, wadanda su ne muhimman ginshikan sauya tsarin ilimi a matakin ƙananan hukumomi.

Sai dai ya nuna damuwa cewa duk da ci gaban da aka samu, har yanzu yara da dama a Jigawa na fuskantar matsaloli wajen samun ingantaccen ilimi saboda talauci, aikatau, aurar da kananan yara ko kuma nisan makaranta daga gida. Ya ce tsarin LESOP zai ba da damar gano wadannan matsaloli a kowane yanki da kuma tsara mafita da suka dace da al’ummar yankin.

Ya kuma bayyana cewa rashin isassun kudade na daga cikin manyan kalubalen da ke hana cimma burin ilimi, tare da bukatar tabbatar da gaskiya wajen amfani da kudaden da aka ware. Ya bukaci gwamnati da ta nemi hanyoyin kirkire-kirkire wajen samar da kudade da kuma tabbatar da cewa kudaden da aka ware don ilimi sun isa makarantu akan lokaci.

 

Usman Muhammad Zaria 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara