Labarai
Mutane Sama Da 100 Sun Mutu A Fadan Da Ya Barke A Sudan
An kwashe sama da makwanni biyu ana gwabza fada tsakanin sojojin Sudan da wata fitacciyar kungiyar sa-kai kan wani babban birnin da ke yammacin yankin Darfur inda aka kashe akalla mutum 123, in ji wata kungiyar agaji ta kasa da kasa a ranar Lahadi.
Yakin da aka yi a el-Fasher, babban birnin lardin Darfur ta Arewa, ya kuma raunata fiye da mutum 930 a lokaci guda, in ji kungiyar likitocin kasa da kasa ta Doctor’s Without Borders.
“Wannan alama ce ta tsananin tashin hankali,” in ji kungiyar. “Muna kira ga bangarorin da ke fada da juna da su kara kaimi wajen kare fararen hula“.
Sabon rikici tsakanin sojoji da dakarun sa-kai ya barke ne a farkon watan nan a birnin, wanda ya tilastawa dubban mutane barin gidajensu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
El-Fasher ya zama cibiyar rikici tsakanin sojoji da RSF, wanda ke samun taimakon mayakan Larabawa da aka fi sani da Janjaweed.
Birnin dai shi ne tunga ta karshe da har yanzu sojoji ke rike da shi a yankin na Darfur.
Rikicin Sudan dai ya faro ne a watan Afrilun bara lokacin da rikici ya barke tsakanin shugabannin sojoji da na RSF a babban birnin kasar, Khartoum, da sauran wurare a kasar.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
