Labarai
‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Matafiya A Jihar Ondo
Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari kan wata motar bas tare da yin garkuwa da wasu matafiya da ba a tantance adadinsu ba a kan babbar hanyar Ikare-Irun Akoko zuwa Ado Ekiti a jihar.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a sansanin noman Oyinmo, daura da Irun Akoko/ Imesi Ekiti a yammacin jiya.
An gano cewa mutanen da aka sace sun fito ne daga yankin Irun akoko, Ikare akoko da Ekiti.
Wata majiya a Irun Akoko ta shaida wa manema labarai cewa a halin yanzu jami’an ‘yan sanda, Sojoji da jami’an Amotekun daga jihohin Ekiti da Ondo tare da hadin gwiwar ‘yan banga na yankin suna toshe dazuzzukan domin ceto wadanda abin ya shafa.
Da take tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, Mrs Funmi Odunlami-Omisanya, ta ce ‘yan sanda na kan gaba a lamarin, duk da cewa ba ta iya tabbatar da adadin wadanda aka sace ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Cov/Leke Adegbite/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
