Labarai
Gwamnatin Kano Ta Ba Ribadu Hakuri Akan Zarginsa Da Hannu A Rikicin Sarauta Na Kano
Gwamnatin Kano ta ba wa Mashawarcin Shugaban Kasa kan sha’anin Tsaro Nuhu Ribadu hakuri kan zargin hannunsa a rikicin masarautun jihar.
Radio Nijeriya ya ruwaito mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam a ranar Asabar yana zargi Ribadu da yunkurin dawo da Alhaji Aminu Ado Bayero kan kujerar Sarkin Kano bayan gwamnatin jihar ta sauke shi tare da sauran sarakunan jihar.
Daga bisani Ribadu ya nesanta kansa da kuma ofishinsa daga rikicin, sannan ya yi barazanar maka mataimakin gwamnan a kotu.
Bayan haka ne mataimakin gwamnan ya ba da hakuri ga Ribadu yana mai cewa yaudarar gwamnatin aka yi da bayanan da aka ba ta.
“Mun kara zurfafa bincike inda kuma gano cewa yaudarar mu aka yi, saboda haka, a madadin gwamnatin Kano, mana ba da hakuri ga Mashawarcin Shugaban Kasa kan Sha’anin Tsaro,” in ji mataimakin gwamnan.
Gwamnatin jihar ta kuma bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya baki kada abin ya kara rincabewa fiye da haka.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
