Ilimi
Talatar Nan Jirgin farko na Maniyatan jihar Kwara Zai Tashi

An dage tashin jirgin farko daga filin jirgin sama na Janar Tunde Idiagbon na kasa da kasa na Ilorin don gudanar da aikin hajjin bana na 2024 zuwa Saudiyya a ranar Talata 21 ga watan Mayu.
Sanarwar da Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kwara, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam ya fitar, ta ce an samu canjin ranar ne sakamakon tsaikon da aka samu daga bangaren NAHCON da kamfanonin jiragen sama.
A cewar sanarwar Alhazan jihar Kwara da farko an shirya yin jigilarsu na farko a ranar Litinin 20 ga Mayu, 2024.
Sanarwar ta shawarci maniyyatan su zo sansanin alhazai litinin din kafin fara jigilar su a ranar Talata da karfe 10:20 na safe.
A halin da ake ciki Mai Martaba Sarkin Ilorin Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya bukaci maniyyatan da su yi amfani da lokacin gudanar da aikin Hajjin bana wajen gudanar da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya, hadin kai da ci gaban tattalin arzikin kasa.
Alhaji Sulu-Gambari ya bayyana haka ne a sakon sa na fatan alheri ta hannun mai magana da yawunsa, Mallam Abdulazeez Arowona.
Ya kuma umarce su da su yi amfani da damar ziyarar da zasu kai garuruwan Madina da Makkah na kasar Saudiyya a wannan lokaci mai albarka a matsayin babban abin alfahari na neman kusanci ga Allah Madaukakin Sarki.
Mai martaba Sarkin ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya ba dukkan alhazai lafiya da basira domin gudanar da ayyukan Hajji cikin nasara.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
