Labarai
Malaman Jihar Jigawa Sun Karrama Shugaban Hukumar Alhazai Ta Jihar
Malaman Kananan hukumomin Jihar jigawa karrama Darakta Janar na Hukumar Jin dadin Alhazan jihar, Alhaji Ahmed Umar Labbo bisa nasarorin da aka samu a aikin hajjin bana.
A lokacin da jagoran Malaman Bitan yake jawabi wajen bikin karramawar da aka gudanar a shelkwatar hukumar dake Dutse babban birnin jihar, Ustaz Sa’idu Aliyu Galamawa ya bayyana cewar, makasudin karramawar shine ganin yadda Darakta Janar na hukumar ya bada gagurumar gudumawa wajen samun nasarar aikin hajjin 2025 a nan gida da kuma kasa mai tsarki.
Ya kara da cewar, sun karrama Labbo ne domin nuna godiya da kuma farin ciki da yadda aikin hajjin bana ya gudana a fannoni dabam dabam.

Shi kuwa Daraktan tsare-tsare na hukumar, Alhaji Muhammad Garba yayi nuni da cewar, wannan shine karon farko da malaman bita suka karrama wani shugaba a tarihin hukumar ta jigawan.
A jawabin sa, Darekta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya nuna farin cikin sa bisa wannan karramanci da malaman bitan suka yi ma shi.
Labbo, ya kuma ta’allaka nasarorin da aka samu a aikin hajjin bana akan hadin kai da goyan bayan Gwamna Umar Namadi.

Yana mai cewar, Gwamna Umar Namadi na sane da irin gudunmawar da malaman bita suka bayar wajen samun nasarar aikin hajjin bana.
Shima a na shi jawabin, Daraktan bincike da kididdiga na hukumar, Alhaji Arab Sabo Aujara ya godewa Malaman bitar bisa gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar aikin hajjin bana.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
