Labarai
Tsaftar Muhalli: An Bukaci Shugabannin Su Yi Koyi da Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu
Daga Usman Muhammad Zaria
An bayyana rashin tsaftar muhalli a matsayin babbar hanyar haddasa matsalolin lafiya a cikin al’umma.
Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Dokta Builder Muhammad Uba, ya bayyana hakan a yayin aikin tsaftar muhalli na kowane wata da aka gudanar a Birnin Kudu.

Shugaban ya sake jaddada jajircewarsa wajen tabbatar da tsaftar muhalli ta hanyar halartar aikin tsaftar muhalli na karshen wata, wanda ake gudanarwa a duk ranar Asabar ta karshe ta kowane wata.
Dokta Muhammad Uba, ya jaddada muhimmancin tsaftar muhalli tare da kira ga al’ummar yankin da su rika tsaftace muhallinsu a kowane lokaci.

Ya bayyana cewa kula da tsaftar muhalli hakki ne da ya rataya a wuyan kowa da kowa domin samar da muhalli mai tsafta da lafiya.
Haka kuma, ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da goyon baya ga shirye-shiryen da ke inganta tsaftar muhalli da kula da lafiyar jama’a.

Builder ya kuma bukaci mazauna yankin da su dauki alhakin kula da muhallinsu tare da yin aiki tukuru domin tsaftace Karamar Hukumar ta Birnin Kudu.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa an gudanar da atisayen tsaftar muhalli na kowane wata a wuraren taruwar jama’a, kasuwanni da unguwanni, inda mahalarta suka bukaci masu ruwa da tsaki su yi koyi da kyakkyawan jagorancin Shugaban Karamar Hukumar tare da ba da fifiko ga tsaftar muhalli.

-
Labarai3 days agoAdalci a Kauru LGA Yayin da Tsarin Raba Mukamai ke Kara Karɓuwa Domin Wakilci Nagari
-
Labarai5 days agoHukumar Alhazan Jihar Jigawa ta Kaddamar da Kwamitin Amirul Hajjin Bana
-
Labarai2 days agoRadio Nigeria @75: Tsohon Dan Jarida Ya Yi Waiwaye Kan Tarihi Radio Nijeriya
-
Labarai7 days agoTrump Ya Aike da Daftarin Shirin Zaman Lafiya ga Iran
-
Labarai2 days agoMasarautar Saminaka ta Bukaci Hadin Kai Don Dorewar Zaman Lafiya a Yankin
-
Labarai2 days agoHukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Kammala Shirin Rigakafi ga Maniyyatan Bana
-
Labarai5 days agoHajjin2026: Jigawa ta Kara Kaimi Wajen Horar Da Maniyyata
-
Labarai2 days agoƊaya Daga Cikin Jariran nan Biyar Ya Rasu, Huɗu Na Ci Gaba Da Jinya a Asibitin Kano
