Kasuwanci
Tarin Bola Na Haddasa Cutuka Ga Mazauna Tudun Ilu A Kaduna
Wani katafaren wurin zubar da shara da aka tanada a wajen Kaduna ya koma wata babbar sana’ar kasuwanci inda ‘yan gwangwan ke amfani da gurbataccen ruwan najasa domin amfanin Noma.
Wata Kungiyar ‘yan jarida ta ziyarci al’ummar Katanga da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna inda aka fara gudanar da wannan aiki inda suka gano cewa kimanin ‘yan gwangwan 150 ne suka tsunduma kansu domin karfafa tattalin arziki a wurin da ake jibge sharar.
Jama’a na yin tururuwa zuwa wurin zubar da sharar na Katanga wanda shi ne babban wurin da gwamnatin jihar ta amince da sharar don tabbatar da tsaftar muhalli.
Mallam Zubairu shi ne shugaba, ya shaidawa tawagar ‘yan jarida da sauran kungiyoyin fararen hula da suka halarci wajen cewa sun fara gano wannan sana’ar ne mai riba fiye da shekaru 3 da suka wuce.
Ya ce suna samar da abin da bai gaza Naira 8,000 kullum, kuma suna biyan N1000 a matsayin haraji ga karamar hukumar.
Mallam Suleiman Kawosu, wanda ya yi tafiyar sama da Kilomita 70 daga Zariya zuwa wurin.
Ya ce yana sayar da wata motar dakon taki a kan kudi da bai gaza Naira 10,000 don ciyar da iyalansa masu ‘ya’ya 9 da kuma kula da su ba, kuma yana jin dadin wannan sana’ar.
A halin da ake ciki kuma tawagar daga baya ta koma Tudun Illu da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa, akwai wani katafaren rumbun da ake zubar da shara ba bisa ka’ida ba da ke da babbar kasuwa a cikin babban birnin jihar.
Da yake magana da tawagar, wani basarake a yankin Alhaji Bala Illu ya koka da cewa wurin da ba a amince da shi ba ya wanzu tsawon shekaru da dama kuma kwanan nan ya haddasa gobara a wata makarantar Firamare da ke kusa.
Don haka ya bukaci gwamnati ta dauki tsattsauran mataki ta hanyar share wurin tare da dakatar da masu aikata wannan aika-aika daga ayyukan da ba su dace ba.
Alhaji Shehu Usman ya tabbatar da abin da basaraken ya fada tun da farko sai dai ya kara da cewa mutane da dama a yankin sun kamu da rashin lafiya sakamakon illar muhalli da sharar ta haifar.
Masana yanayi irin su Gloria Kasang Bulus da Zinta Istifanus sun koka kan yadda ake samun juji a tsakiyar wuraren zama a Kaduna.
Ziyarar da ‘yan jarida da masu kula da muhalli suka yi ta rangadin wuraren zubar da ruwa na najasa ya kasance irinsa na farko don samun bayanai na farko kan batutuwan da suka shafi muhalli da sauyin yanayi domin su adana bayanansu da kuma bayar da rahoto ga masu iko kan bin kyawawan halaye na muhalli na duniya.
Cov/Shindong Bala/Wababe
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
