Labarai
Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo
Daga Abdullahi Jalaluddeen
Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki 257 da aka sata a wani aikin tsaro na haɗin gwiwa a Ƙaramar Hukumar Gwarzon Jihar Kano.
An gudanar da aikin ne ta haɗin gwiwar rundunar tsaro karkashin Bataliya ta 3, bayan samun kiran gaggawa daga mazauna yankin.
Mataimakin Daraktan Harkokin Yada Labarai na Soji, Majar Babatunde Zubair, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Kano.
Ya ce rundunar tsaron ta samu kiran gaggawa ne da misalin ƙarfe 6 na safe ranar 1 ga watan Maris, inda suka garzaya inda lamarin ya faru nan take.
A cewarsa, sojojin sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar inda suka samu nasarar dawo da dabbobin da aka sata, waɗanda suka haɗa da Shanu, Awakai da Jaki guda daya.
Manjo Zubair ya ƙara da cewa an mika dabbobin da aka dawo da su ga masu su, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin bin sawu don kamo ‘yan bindigarda suka tsere.
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
