Labarai
Shirin Soil Values Da NAIDA Sun Fito Da Tsarin Saukaka Samun Kayayyakin Gona Ga Manoma
Shirin Inganta Noma da Kula da Sauyin Yanayi na Soil Values, tare da haɗin gwiwar Kungiyar Dillalan Kayayyakin Aikin Gona ta Kasa (NAIDA) ta Arewa maso Yamma, ya ƙaddamar da sabon tsari domin sauƙaƙa samun kayayyakin gona ga ƙananan manoma a yankunan Arewacin Najeriya, da ake kira “one-stop shop a turance.
Jami’ar shirin ta kasa Misis Medina Ayuba Fagbemi, ta bayyana cewa za a samar da shagunan tafi-da-gidanka guda tara da za su kai kayayyaki zuwa sama da al’ummomi 20 a jihohin Kano, Jigawa da Bauchi, inda ake sa ran shirin zai amfanar da kusan ƙananan manoma 7,000.

Ta ce tsarin zai taimaka wajen kusantar da ingantattun iri, taki da magungunan kashe kwari ga manoma, tare da samar da shawarwari na gona, gwajin ƙasa da kuma tantance bayanan manoma ta yanar gizo.
Misis Medinat Fagbemi ta yaba wa manoma da malaman gona da suka amince da wannan tsari, tana ƙarfafa su da su yi aiki da gaskiya da tare da jajircewa.

A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban kungiyar NAIDA Arewa maso Yamma, Injiniya Abdullahi Muhammad, ya shawarci wadanda suka ci gajiyar shirin da su aiwatar da horon da suka samu yadda ya kamata, yayin da Daraktan Hukumar Sauya Fasalin Noma ta Jigawa, Dr. Saifullahi Umar, ya tabbatar da goyon bayan gwamnatin jihar domin cimma nasarar shirin.

Shirin Soil Values, wanda gwamnatin kasar Netherlands ke tallafawa da Yuro Miliyan 100 na tsawon shekaru goma, an kirkiro sa ne da nufin farfaɗo da ƙasar noma, rage gibin amfanin gona, da farfado da ƙasar da ta lalace a Najeriya da wasu ƙasashen Yammacin Afirka.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
