Labarai
NIPHID ta gudanar da gangamin wayar da kai kan tarin fuka a Zaria, Kaduna
Cibiyar kula da lafiya dake Saye Zaria, ta gudanar da gangamin wayar da kai kan cutar tarin fuka (TB) a masallatan Juma’a da coci-coci, tare da gudanar da shirin jinya kyauta a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko (PHC) ta Chikaji, a ƙaramar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.
Gangamin na daga cikin shirin wayar da kai domin ƙara fahimtar jama’a kan hanyoyin kariya, gano cutar da wuri, da kuma maganinta, tare da ƙarfafa shigar al’umma cikin yaki da cutar.
Da yake jawabi yayin aikin, Darakta-Janar na Cibiyar, Dakta Abdullahi Dalhatu Aminu, ya bayyana kwarin gwiwa cewa za a iya kawar da tarin fuka idan dukkan masu ruwa da tsaki suka tashi tsaye wajen yakar ta.
Ya jaddada cewa kawar da cutar na bukatar haɗin kai tsakanin gwamnati, al’umma da kuma daidaikun mutane, yana mai cewa nasara za ta samu ne idan kowa ya taka rawarsa.
Dakta Abdullahi ya bayyana cewa gwamnati na bayar da magungunan tarin fuka kyauta, tare da gwaje-gwaje da sauran hanyoyin gano cutar a sassa daban-daban na ƙasar.
Sai dai ya ce har yanzu wasu marasa lafiya na fuskantar ƙalubale wajen samun cibiyoyin lafiya sakamakon matsalar sufuri da sauran buƙatun yau da kullum.
Ya ƙara da cewa Najeriya ce ta huɗu a duniya wajen yawan masu dauke da tarin fuka, kuma ta farko a nahiyar Afirka, lamarin da ya bayyana a matsayin babban ƙalubale na lafiya da ke bukatar gaggawar magancewa.
Ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kai, tare da neman goyon bayan jama’a da hukumomi ta hanyar tallafi da shawarwari domin kawo ƙarshen cutar a Najeriya.
Haka kuma, wata kwararriyar likita, Dakta Umma Aliyu, wacce ke kula da sashen kula da marasa lafiya, ta ce tarin fuka cuta ce mai warkewa kuma mai hana yaɗuwa idan aka bi matakan kariya da suka dace.
Ta bayyana cewa kariya daga cutar na bukatar guje wa cunkoson jama’a da kuma tabbatar da samun iska mai kyau a gidaje da wuraren taruwar jama’a.
Dakta Aliyu ta kuma shawarci mutane da su guji shan taba sigari da yawan shan giya, tana mai cewa waɗannan halaye na ƙara haɗarin kamuwa da tarin fuka.
Wasu daga cikin marasa lafiyar tarin fuka da suka halarci shirin sun nuna godiya ga National Institute of Public Health and Infectious Diseases bisa shirya wannan gangamin wayar da kai.
Rahoton Radio Nigeria ya ce yayin gangamin, ƙwararru sun shafe wani ɓangare na rana a PHC Chikaji inda aka gudanar da gwaje-gwaje da shawarwari kyauta ga mutane da dama, ciki har da yara da manya.
Ibrahim Suleiman/Zaria
-
Labarai3 days agoAdalci a Kauru LGA Yayin da Tsarin Raba Mukamai ke Kara Karɓuwa Domin Wakilci Nagari
-
Labarai5 days agoHukumar Alhazan Jihar Jigawa ta Kaddamar da Kwamitin Amirul Hajjin Bana
-
Labarai2 days agoRadio Nigeria @75: Tsohon Dan Jarida Ya Yi Waiwaye Kan Tarihi Radio Nijeriya
-
Labarai7 days agoTrump Ya Aike da Daftarin Shirin Zaman Lafiya ga Iran
-
Labarai7 days agoGwamnatin Kano ta Samar da Babura Don Inganta Yaki da Cutar Tarin Fuka a Karkara
-
Labarai2 days agoMasarautar Saminaka ta Bukaci Hadin Kai Don Dorewar Zaman Lafiya a Yankin
-
Labarai5 days agoHajjin2026: Jigawa ta Kara Kaimi Wajen Horar Da Maniyyata
-
Labarai2 days agoHukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Kammala Shirin Rigakafi ga Maniyyatan Bana
