Connect with us

Labarai

Minista Goronyo ya Duba Ci Gaban Aikin Titin Abuja Zuwa Kano

Published

on

Ministan Kasa a Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, Bello Muhammad Goronyo, ya sake jaddada kudirin Gwamnatin Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu na tabbatar da kammala aikin gyaran titin Abuja zuwa Kaduna har zuwa Kano, da kuma wasu manyan tituna a Arewacin ƙasar nan.

Ministan, Barrister Bello Goronyo (ESQ), ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara don duba yadda aikin ke gudana, domin tabbatar da cewa ana sa idanu sosai, kuma ‘yan kwangila suna gudanar da aikin cikin inganci da nagarta.

Ministan ya fara duba aikin tun daga Tungan Maje, Madalla, Zuma Resort, Sabon Wuse, Jere, Abuja Junction, Gwanin Gora, sannan ya ci gaba zuwa Zaria har zuwa Kano, inda aikin ke ci gaba yadda ya dace.

Haka kuma, Ministan ya ja kunnen kamfanin da ke gudanar da aikin  daInfiouest International Limited da ya tabbatar sun kammala aikin kafin karshen shekarar 2026, kamar yadda Shugaban Kasa ya bayar da umarni.

Barrister Bello Muhammad Goronyo ya bayyana cewa Shugaban Kasa Tinubu na da damuwa matuƙa kan wahalar da matafiya ke sha wajen amfani da wannan hanyar, wanda hakan yasa gwamnati ta maida hankali sosai kan aikin.

A cewar Ministan, kamfanonin sun riga sun yi alkawarin kammala aikin a kan lokaci tare da tabbatar da ƙyakykyawan aiki kamar yadda aka shimfiɗa ka’idoji.

Wannan ziyarar duba aikin dai an gudanar da ita ne bisa umarnin Shugaban Kasa ga Ministan Kasa na aikin, Honourable Bello Muhammad Goronyo (ESQ), domin tabbatar da cewa aikin yana tafiya yadda ya kamata ba tare da tangarda ba.

Kaura Namoda/ Wababe

Labarai

Labarai9 hours ago

Tinubu Ya Nada Ibrahim Masari a Matsayin Mai Ba Shi Shawara Kan Harkokin Siyasa

Daga Bello Wakili Shugaban Ƙasa Bola Tinubu  ya naɗa Ibrahim Aminu Masari a matsayin Mai ba shi Shawara na Musamman...

Labarai10 hours ago

Kungiyoyin Alumma a Jigawa Sun Bayyana Goyon Bayansu ga Gwamna Namadi Kan Lamarin Walida Abdulhadi

Daga Usman Muhammad Zaria  Wata ƙungiyar al’umma mai suna Hadejia Advocacy ta yaba wa Gwamnan  Jigawa, Umar Namadi, kan yadda...

Labarai16 hours ago

Ramadan: Sarkin Kauru Ya Bukaci a Kara Karfafa Tsoro Tare da Tallafawa Marasa Galihu

Daga Yusuf Zubairu Kauru Sarkin Kauru da ke Jihar Kaduna, Alhaji Zakari Ya’u Shehu Usman, ya yi kira da a...

Labarai16 hours ago

Gwamnatin Jigawa Ta Sha Alwashin Bin Kadin Shari’ar Walida Abdulhadi

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamna Umar Namadi ya tabbatar da cewa Gwamnatin  Jigawa za ta bi sawun shari’ar sace ‘yar...

Labarai2 days ago

Ana Zargin Mutum 140 Sun Bace Bayan Nutsewar Jirgin Ruwan Iran a Gaɓar Sri Lanka

Rundunar sojin ruwan Sri Lanka ta tabbatar da ceto mutum 32 bayan samun kiran gaggawa daga jirgin ruwan sojin Iran...

Ilimi2 days ago

Gwamnatin Tarayya da ke Gusau za ta Kafa Cibiyar Nazari kan Tarihi da Al’adun Zamfara

Daga Aminu Dalhatu  Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Gusau (FUGUS), Farfesa Tukur Adamu, ya sanar da shirin jami’ar na kafa...

Labarai2 days ago

Jam’iyyar APC Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni a Jihar Kano

Daga Abdullahi Jalaluddeen Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Kano ta zaɓi sabbin shugabanni domin jagorantar harkokin jam’iyyar. Zaɓen,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Miliyoyin Naira Don Sayen Gidaje 96 Daga Gwamnatin Tarayya

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Miliyan 853 domin sayen gidaje guda...

Labarai3 days ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai4 days ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Mafi Shahara