Connect with us

Labarai

Matasan Kauru Sun Yi Allah-wadai da Mulkin Ƙarfi, Sun Buƙaci Adalci da Haɗin Kai

Published

on

 

Daga Yusuf Zubairu

Wata ƙungiyar matasa a Ƙaramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna ta bayyana cewa shugabanci na bai-ɗaya ba tare da nuna rinjaye a bangare daya ba, shi ne ginshikin dorewar dimokuraɗiyya da haɗin kan al’umma a yankin.

Ƙungiyar, wato Kauru Youth Ambassadors (KYA) ta yi wannan kira ne yayin mayar da martani ga kalaman wani mai suna Musa Waziri ne a wani bidiyo da ya karade kafafen yanar gizo, inda ta jaddada cewa Kauru ta ƙunshi sassa uku ne da suka hada da  Masarautar Kauru, Sarautar Kumana da Sarautar Chawai.

A cewar ƙungiyar, kowanne daga cikin waɗannan sassa uku na da masu ilimi, ƙwarewa da kishin ƙasa, waɗanda suka cancanci rike muƙamai a kowane fanni.

Da yake magana a madadin KYA, Kwamared Junaidu Ishaq Maisalati ya ce ƙungiyar ta soki ikirarin Waziri na cewa “ana ƙwace iko ne, ba a bayar da shi ba,” inda ya bayyana cewa mafi akasari  siyasa na karkata ne ga waɗanda ke da rinjayen yawan jama’a, da albarkatun kasa da damar shiga tsarin jam’iyya.

Ya bayyana cewa tsarin raba mulki (zoning) ba wajibi ba ne a harkar siyasa, illa hanya ce ta kaucewa watsi da wani yanki, tare da tabbatar da wakilci na adalci a al’umma mai bambance-bambance kamar Kauru.

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa ba daidai ba ne a ce tsarin karba-karba wato zoning na haifar da shugabanni marasa ƙwarewa, alhali kuma ana da tabbacin cewa akwai ƙwararru a dukkan sassan Kauru.

Ta jaddada cewa tsarin na karba-karba ba ya rage ƙa’idar shugabanci, sai dai yana ƙarfafa kowanne yanki ne ya gabatar da mafi cancantar ’ya’yansa idan aka ba shi dama.

A cewar ƙungiyar, mulki na karba karba  yana ƙarfafa tarbiyyar shugabanci, gina ƙwarewa da kuma ƙarfafa cibiyoyin siyasa.

Saboda haka, ta yi gargaɗi cewa ci gaba da keɓance wasu sassa na iya haifar da rashin yarda, sakaci da ɓacin rai, wanda hakan ke tauye ci gaba da haɗin kan al’umma.

Ƙungiyar Kauru Youth Ambassadors (KYA) ta nanata cewa ya zama wajibi a tabbatar da adalci domin samun haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a Kauru.

Labarai

Ilimi15 hours ago

Dr. Builder Muhammad Uba Ya Jagoranci Rangadin Makarantu a Birnin Kudu

Daga Usman Muhammad Zaria Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dakta Builder Muhammad Uba ya bayyana ilimi a...

Labarai2 days ago

Masarautar Saminaka ta Bukaci Hadin Kai Don Dorewar Zaman Lafiya a Yankin

Daga Yusuf Zubairu Majalisar Masarautar Saminaka da ke Jihar Kaduna ta yi kira ga al’ummomin da ke Karamar Hukumar Lere...

Labarai2 days ago

Hukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Kammala Shirin Rigakafi ga Maniyyatan Bana

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta kammala tanadin katin shaidar rigakafin cututtuka ga dukkan maniyyatan aikin Hajjin shekarar...

Labarai2 days ago

NEMA ta Karbi ‘Yan Najeriya 522 da Aka Dawo da su Daga Jamhuriyar Nijar

Daga Khadijah Aliyu Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta karɓi wani rukuni na ’yan Najeriya 522 da...

Labarai2 days ago

Za mu kai hari kan gidajen jami’an Amurka da Isra’ila – Iran

Hedikwatar Khatam al-Anbiya, wacce ita ce babbar cibiyar da ke kula da daidaita ayyukan rundunonin sojin Iran, ta yi barazanar...

Labarai2 days ago

Radio Nigeria @75: Tsohon Dan Jarida Ya Yi Waiwaye Kan Tarihi Radio Nijeriya

An bayyana cikar shekaru 75 da kafuwar Radio Nigeria a matsayin wani babban mataki wajen gina ci gaban zamantakewa, tattalin...

Labarai2 days ago

Ɗaya Daga Cikin Jariran nan Biyar Ya Rasu, Huɗu Na Ci Gaba Da Jinya a Asibitin Kano

Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar ɗaya daga cikin jarirai biyar da aka haifa a Asibitin...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Sadaukar Da Albashinsa Domin Sabon Asusun Tallafi Ga Sojoji

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kafa wani asusun tallafi na musamman domin taimaka wa jami’an rundunar sojin...

Labarai2 days ago

FMC Gusau ta karɓi tallafin littattafan lafiya daga gidauniyar Sir Emeka Offor

Asibitin Kula da Lafiya na Tarayya da ke Gusau, ya karɓi tarin littattafan kiwon lafiya da mujallu daga Sir Emeka...

Labarai2 days ago

NIPHID ta gudanar da gangamin wayar da kai kan tarin fuka a Zaria, Kaduna

Cibiyar kula da lafiya dake Saye Zaria, ta gudanar da gangamin wayar da kai kan cutar tarin fuka (TB) a...

Mafi Shahara