Labarai
Majalisar Dattijan Na So A Bai Wa Kananan Hukumomi Yancin Kai
Majalisar Dattijan Najeriya ta nemi Shugaba Tinubu ya shige gaba domin nema wa kananan hukumomi ‘yanci a wajen jihohi, wanda suka ce hakan zai iya magance matsalar tsaro da ake fama da ita da tururuwar da mutane ke yi zuwa birane da kuma rashin aikin yi.
Sanata Abdurrahaman Kawu Sumaila ne ya gabatar da kudurin wanda ya ce akwai bukatar a zauna da gwamnoni da masu ruwa da tsaki domin tattauna yadda za a yi kananan hukumomi su samu ‘yancinsu da suka rasa a baya.
Kawu Sumaila ya ce a wannan lokacin za a samu nasara saboda salon da majalisar ta dauka a wannan karon ya sha banban da matakan da aka rika dauka a baya.
Sanatan ya ce sun nemi shugaban kas aya shige gaba wajen tabbatar da an samu abinda ake so, ta hanyar kiran taron masu ruwa da tsaki da zai kunshi gwamnoni da ýan majalisu na tarayya da na jihohi da shugabannin al’umma da malaman addini da sauransu domin a tattauna domin samarwa kananan hukumomi matsaya guda.
Kawu Sumaila ya ce idan har aka samu nasarar daukar matakin za a samu saukin rashin tsaro da talauci da ya addabi jihohin arewacin Najeriya, ” A cikin wata uku abubuwa za su canja, idan aka ce a karamar hukuma za a yi tasarrafin miliyan 300 ko miliyan 400, bayan an biya ma’aikata duk wasu kananan ayyuka za a yi.”
Sanata Kawu ya ce ba abin birgewa ba ne ace anyi zabe amman jam’iya guda za ta lashe zaben kananan hukumomi ” kai an zabe ka, yan majalisar jihohin ka daga jam’iyu daban-daban, amman ranar zaben kananan hukumomi jam’iya guda za ta lashe, kai kasan ba gaskiya ake yi ba”.
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
