Labarai
Majalisar Dattawa Ta Amince da Karbo Rancen Naira Tiriliyan 1.15 Domin Cike Gibin Kasafin Kudi
Daga Bashir Meyere
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da bukatar Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, na neman rancen Naira Tiriliyan 1.15 domin cike gibin kasafin kudin shekarar 2025.
Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da lamuran bashi na cikin gida da na waje.
Yayin da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Magatakarda Wamako, wanda mataimakinsa Sanata Haruna Manu ya wakilta, ya bayyana cewa kasafin kudin shekarar 2025 na Naira tiriliyan 59.99 da Majalisar ta amince da shi, ya karu da Naira tiriliyan 5.25 idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 54.74 da gwamnatin tarayya ta fara gabatarwa.
Ya ce an riga an amince da Naira tiriliyan 12.95 a cikin kasafin, wanda hakan ya bar gibin Naira tiriliyan 1.147, abin da ya haifar da bukatar wannan shirin neman rance.
Kwamitin ya bai wa Majalisar shawarar amincewa da rancen cikin gida na Naira tiriliyan 1.15 domin cike gibin da ya samo asali daga karin kudin kasafin.
Kwamitin ya kuma bukaci Ministar Kudi da Ofishin Kula da Lamuran Bashi su tabbatar da cewa an aiwatar da rancen cikin tsari, tare da bin ka’idojin gaskiya, da sharuɗɗan da suka dace.
Majalisar Dattawa ta kuma umurci kwamitinta mai kula da bashin cikin gida da na waje da ya rika sa ido kan yadda za a aiwatar da amfani da kudin da aka ciwo bashi.
Haka kuma, Ministar Kudi za ta rika mika rahoton kowane watanni uku kan halin da ake ciki, da amfani da kudaden, da yadda ake biyan basussuka, yayin da za a kai duk wani rahoton sabawa tsarin ga Majalisar Dattawa domin daukar matakin doka da ya dace.
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
