Labarai
Ma’aikatar Lafiya Ta Fara Daukar Jami’an Kula da Lafiya na Ƙasa a Jigawa
Usman Muhammad Zaria
Ma’aikatar Lafiya ta kasa karkashin shirin kula da lafiya na SWAP ta fara aikin daukar Jami’an Kula da Lafiya na Ƙasa wato (National Health Fellows) a Jihar Jigawa.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan kammala aikin, Mataimakin Darakta kuma Mai Taimaka wa Darakta-Janar na Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa, Dakta Jibrin Muhammad Bashar, ya bayyana cewa aikin daukar ma’aikatan wani shiri ne na Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya karkashin jagorancin Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate.

Dakta Bashar, wanda kuma shi ne Babban Mai Kula da aikin daukar ma’aikatan a Jihar Jigawa, ya bayyana cewa shirin na da nufin zaben Jami’an Kula da Lafiya na Ƙasa da za su rika sa ido kan aiwatar da Asusun Kula da Lafiya na Asali (Basic Health Care Provision Fund) a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a fadin jihar.

A cewarsa, wadannan ma’aikata za su kasance jakadu na Asusun Kula da Lafiya na Gwamnatin Tarayya, wanda Hukumar Kula da Kiwon Lafiya ta Matakin Farko ta Kasa (National Primary Health Care Development Agency) ke kula da shi.

Ya kara da cewa an kirkiri asusun ne domin tallafa wa rukunin al’umma masu rauni, ciki har da mata, yara da tsofaffi, ta hanyar samar da muhimman ayyukan kiwon lafiya da kuma tallafin kudi.

Ya bayyana cewa za a zabi mutum ashirin da bakwai, inda kowane daya zai wakilci daya daga cikin kananan hukumomi ashirin da bakwai na Jihar Jigawa.
Dakta Bashar ya nuna gamsuwa da yadda aka gudanar da aikin daukar ma’aikatan, inda ya yaba wa kwamitin daukar ma’aikata na jihar da kwamitin bisa kwarewa, gaskiya da kuma rashin nuna bangaranci yayin aikin.
-
Labarai3 days agoAdalci a Kauru LGA Yayin da Tsarin Raba Mukamai ke Kara Karɓuwa Domin Wakilci Nagari
-
Labarai5 days agoHukumar Alhazan Jihar Jigawa ta Kaddamar da Kwamitin Amirul Hajjin Bana
-
Labarai2 days agoRadio Nigeria @75: Tsohon Dan Jarida Ya Yi Waiwaye Kan Tarihi Radio Nijeriya
-
Labarai7 days agoTrump Ya Aike da Daftarin Shirin Zaman Lafiya ga Iran
-
Labarai2 days agoMasarautar Saminaka ta Bukaci Hadin Kai Don Dorewar Zaman Lafiya a Yankin
-
Labarai2 days agoHukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Kammala Shirin Rigakafi ga Maniyyatan Bana
-
Labarai5 days agoHajjin2026: Jigawa ta Kara Kaimi Wajen Horar Da Maniyyata
-
Labarai2 days agoƊaya Daga Cikin Jariran nan Biyar Ya Rasu, Huɗu Na Ci Gaba Da Jinya a Asibitin Kano
