Connect with us

Labarai

Za Mu Yaki Ayyukan Ta’addanci A Jihar Kano – Sabon Kwamishina

Published

on

Kwamishinan ‘yan sanda na  Jihar Kano CP Salman Dogo Garba, ya fara sintiri a yankunan da ‘yan daba suka sake kunno kai a wasu sassan birnin Kano, tare da tabbatar wa mazauna yankunan kudurinsa na wanzar da zaman lafiya.

CP Dogo Garba ya nemi hadin kan shugabannin al’umma da jami’an ‘yan sanda na yanki (DPOs) don tsara dabarun yakar wannan barazana da kuma dawo da tsaro.

Ya jaddada cewa tsaro hakki ne ya rataya a wuyan kowa, don haka ya bukaci jama’a da su kai rahoton duk wata barazana da ka iya kunno kai ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su ko kuma ta lambobin gaggawa.

CP ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, kuma ana kokarin kamo masu aikata laifin da masu daukar nauyinsu.

Ya yaba da goyon bayan mazauna yankin masu son zaman lafiya, inda ya  bukaci a ci gaba da ba da hadin kai.

Abdullahi Jalaluddeen

Labarai

Labarai10 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara