Labarai
Kwamishinan ‘Yan Sanda Na Jihar Kano Ya Sha Alwashin Kawar Da Badala A Harkokin Fina-finai
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cikakken goyon bayan rundunar ‘yan sanda ga Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano wajen tabbatar da kiyaye dabi’u da yakar munanan halaye a cikin al’umma.
CP Bakori ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar wayar da kai da Sakatare na Hukumar, Abba El-Mustapha, ya kai tare da tawagarsa zuwa hedikwatar rundunar ‘yan sandan Kano.
A yayin ganawar, CP Bakori ya yaba da jagorancin hukumar, musamman kokarin da El-Mustapha ke yi wajen tsara harkokin masana’antar Kannywood da kuma kare tarbiyya ta hanyar sa ido mai tsauri.
Ya tabbatar da ci gaba da hadin gwiwa tsakanin rundunar da hukumar, musamman wajen dakile cin zarafi da amfani da kafafen sada zumunta wajen yada munanan abubuwa da kuma kare mutuncin jama’a.

“Rundunar ‘yan sanda a Kano za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da hukumar domin tabbatar da doka da oda da kuma kare tarbiyya a kananan hukumomi 44 na jihar.” In ji CP Bakori.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Tace Fina-finai, Abba El-Mustapha, ya taya CP Bakori murna bisa sabon nadin da aka masa, tare da jaddada bukatar hadin gwiwa mai karfi tsakanin ‘yan sanda da hukumar.
Ya ce tsaftace fina-finai da sauran abubuwan da ke shafar kafafen watsa labarai ba zai yiwu ba sai da goyon bayan hukumomin tsaro.
“Muna daraja hadin gwiwarmu da rundunar ‘yan sanda, wanda hakan ya taimaka mana wajen tabbatar da bin ka’ida da kare dabi’u a jihar Kano.” In ji El-Mustapha.
Ya kuma gode wa kwamishinan bisa kyakkyawar tarba da kuma jajircewarsa wajen goyon bayan aikin hukumar, yana mai jaddada kudirin hukumar na ci gaba da sa ido a kafafen watsa labarai da fina-finai, daidai da al’adu da dabi’un al’ummar Kano.
Khadijah Aliyu
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
