Connect with us

Labarai

Jihohin Jigawa, Katsina Da Kano Za Su Kaddamar Da Asusun Wutar Lantarki Mafi Girma A Najeriya

Published

on

Jihohin Jigawa, Katsina da Kano sun amince da hadin gwiwa kan kasuwar wutar lantarki ta jihohi uku, tare da samun kaso a kamfanin Future Energies Africa (FEA), wanda shi ne ke da hannun  jari mafi girma a Kano Electricity Distribution Company (KEDCO).

Kwamishinan wutar lantarki na jihar Jigawa, Injiniya Surajo Musa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse.

Ya ce gwamnonin jihohin ukun sun cimma wannan matsaya ce a birnin Marrakech, kasar Morocco, yayin taron kolin manyan jami’ai kan samar da wutar lantarki.

Injiniya Surajo Musa ya kara da cewa a yayin taron, jihohin Kano da Katsina sun amince da yin hadin gwiwa da jihar Jigawa wajen samun kaso a Future Energies Africa, domin karfafa tsare-tsaren ci gaban KEDCO.

Jihohin uku tare da kamfanin Future Energies Africa za su kaddamar da wani asusun samar da wutar lantarki na musamman  wanda shi ne irinsa na farko  da ake sa ran zai kai Naira Biliyan 50 a matakin farko, domin hanzarta samar da wuta a cikin jihohin uku,” in ji shi.

Sanarwar ta kara da cewa jihohin za su duba hanyoyin da Dokar Wutar Lantarki (Electricity Act) ta tanada, domin yin hadin gwiwa kan kasuwar wutar lantarki ta jihohin uku, inda kowanne zai amfana.

Ya ce FEA tare da gwamnonin jihohin uku za su rika gudanar da taron kasa da kasa sau daya a shekara, sannan su rika ganawa duk bayan watanni uku domin duba ci gaba da karfafa dangantakar kasuwar wutar lantarki ta Arewa maso Yamma.

 

Usman Mohammed Zaria

 

 

Labarai

Labarai2 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai22 hours ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai1 day ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai1 day ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai1 day ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara