Labarai
Hukumar Alhazan Jihar Jigawa ta Kaddamar da Kwamitin Amirul Hajjin Bana
Daga Usman Mohammed Zaria
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta kaddamar da kwamitin Amirul Hajj na bana karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Hameem Nuhu Muhammadu Sanusi.
A Jawabin sa wajen kaddamar da kwamitin, Darakta Janar na Hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce tuni hukumar Alhazai ta jihar ta kammala duk wani shiri da yakamata domin tunkarar aikin hajjin bana.

Yana mai cewar sun samar da masaukai ga maniyyata a kusa da harami kuma masu inganci, yayin da ake ci gaba da bita ga maniyata domin ilmantar da su dokokin aikin hajji.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce a bana hukumomin Saudiya sun fito da tsarin cewar sai maniyaci yana da koshin lafiya za’a bari ya sauke farali.


Alhaji Ahmed Labbo, ya kuma bayyana cewar a bara hukumar ta samu lambobin yabo sakamakon ficen da tayi a aikin hajjin 2025. Yana mai fatan a bana za’a samu karin lambobin yabo a yayin gudanar da aikin hajjin.
A jawabinsa, Amirul hajjin kuma mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Hameem Muhammadu Sunusi ya bada tabbacin yin duk abin da ya dace domin samun nasarar gabatar da aikin hajjin bana.


Kazalika, ya kuma yi fatan kwamitin zai yi aiki tare da ma’aikatan hukumar domin samun nasarar da ake bukata, kasancewar Darakta janar na hukumar kwararre ne a wannan aiki.

-
Labarai3 days agoAdalci a Kauru LGA Yayin da Tsarin Raba Mukamai ke Kara Karɓuwa Domin Wakilci Nagari
-
Labarai2 days agoRadio Nigeria @75: Tsohon Dan Jarida Ya Yi Waiwaye Kan Tarihi Radio Nijeriya
-
Labarai7 days agoTrump Ya Aike da Daftarin Shirin Zaman Lafiya ga Iran
-
Labarai7 days agoGwamnatin Kano ta Samar da Babura Don Inganta Yaki da Cutar Tarin Fuka a Karkara
-
Labarai2 days agoMasarautar Saminaka ta Bukaci Hadin Kai Don Dorewar Zaman Lafiya a Yankin
-
Labarai5 days agoHajjin2026: Jigawa ta Kara Kaimi Wajen Horar Da Maniyyata
-
Labarai2 days agoHukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Kammala Shirin Rigakafi ga Maniyyatan Bana
-
Labarai2 days agoƊaya Daga Cikin Jariran nan Biyar Ya Rasu, Huɗu Na Ci Gaba Da Jinya a Asibitin Kano
