Connect with us

Labarai

Hukumar Alhazai Ta Kasa Ta Sanar Da Kudin Aikin Hajjin Bana

Published

on

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da kudin aikin Hajjin shekarar 2025.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun
Mataimakiyar Daraktan Watsa Labarai ta hukumar, Fatima Sanda Usara.

Ta ce “Hukumar aikin Hajji ta kasa (NAHCON), a karkashin jagorancin shugabanta, Farfesa Abdullahi Saleh Usman na farin cikin sanar da kudin aikin Hajjin shekarar 2025”.

Ta ce an sanar da kudin kujerar na bana ne bayan amincewar ofishin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.

Ta kara da cewa “Hakika Shugaban Hukumar NAHCON da tawagarsa tare da hadin guiwar wakilin fadar shugaban kasa, Malam Ameen Amshi, wanda shi ne mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan ayyuka na musamman, sun yi  kokari matuka wajen ganin an biya kudin aikin Hajji daidai da yadda aka biya a bara.

“Maniyyata aikin Hajjin 2025 daga shiyyar Borno da Adamawa, za su Naira miliyan 8,327,125.59 (miliyan takwas, da dubu dari uku da ashirin da bakwai, da dari daya da ashirin da biyar da kwabo hamsin da tara).

“Hakazalika, maniyyata daga jihohin Kudu za su biya Naira miliyan 8, 784, 085.59 (miliyan takwas, da dubu dari bakwai da tamanin da hudu, da Naira tamanin da biyar Naira kobo hamsin da tara).

“Alhazan da suka fito daga shiyyar Arewa kuma za su biya Naira 8, 457,685.59 (miliyan takwas, da dubu dari hudu da hamsin da bakwai, da dari shida da tamanin da biyar da kwabo hamsin da tara).”

Fatima Usara ya ce Farfesa Saleh ya yaba wa daukacin tawagar, inda ya bayyana kudin aikin Hajjin a matsayin wani babban hadin gwiwa da duk masu ruwa da tsaki.

Ya yaba da goyon bayan fadar shugaban kasa da kungiyar sakatarorin gudanarwa na jihohi.

Shugaban ya bukaci maniyyatan da suke son zuwa aikin Hajji da su lura da ka’idoji hukumar da na kasar Saudiyya, tare da jaddada mahimmancin biyan kudi da wuri da kuma yin rajista a kan lokaci don guje wa matsaloli.#Hajj2024

 

Safiyah Abdulkadir

Labarai

Labarai9 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara