Labarai
Gwamnatin Zamfara ta Bada Babura 10 ga ‘Yan Sanda a Jihar Domin Inganta Tsaro
Daga Aminu Dalhatu
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayar da sabbin babura guda goma domin ayyukan tsaro ga Ofishin ’Yan Sanda na Gusau ta Tsakiya da nufin ƙarfafa sintiri da inganta tsaro a cikin babban birnin jihar.
An mika baburan ga DPO na ofishin ‘Yan Sanda da ke Gusau ta Tsakiya, CSP Abubakar Sani Muhammad, ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Mohammad Nakwada.

Wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai a Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Sulaiman Ahmad Tudu, ya fitar, ta bayyana cewa Sakataren Gwamnatin ya samu wakilcin Babban Sakataren Harkokin Majalisar Zartarwa Dakta Abubakar Mohammad Gusau.
Malam Nakwada ya bayyana cewa an bayar da baburan ne domin inganta ayyukan ’yan sanda, musamman a wuraren da ba su da sauƙin shiga da motocin sintiri.

Ya kuma ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa Ofishin ‘Yan Sandan ta hanyar samar da man fetur da za su rika amfani da shi a ababen hawansu domin tabbatar da ingantaccen aiki da dorewar hidimar tsaro.
A cewarsa, wannan tallafi na daga cikin ƙudirin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal na yaƙi da dukkan nau’ikan ayyukan ta’addanci da kuma ƙarfafa tsaro a fadin Jihar Zamfara.

Da yake karɓar Baburan a madadin Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya, DPO CSP Abubakar Sani Mohammad ya nuna godiyarsa ga gwamnatin jihar, inda ya ce Baburan za su ƙara wa sashen ƙarfi wajen tinkarar masu aikata laifuka da ke amfani da wurare masu wahalar shiga wajen aikata ayyukan ta’addanci.
Ya yabawa Gwamna Dauda Lawal bisa ci gaba da ba hukumomin tsaro tallafi, tare da tabbatar da kara jaddada cewa za su ci gaba da sauke nauyin da aka dora musu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
A wani labari mai nasaba da hakan, gwamnatin jihar na ci gaba da gyarawa da sake fasalin Ofishin ’Yan Sanda na Gusau ta Tsakiya da kuma Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Zamfara, akan kudi kuɗaɗe kimanin Naira Miliyan 726 da dubu 900 na ofishin Gusau ta Tsakiya, da kuma Naira biliyan 1 da miliyan 400 a hedikwatar.
-
Labarai3 days agoAdalci a Kauru LGA Yayin da Tsarin Raba Mukamai ke Kara Karɓuwa Domin Wakilci Nagari
-
Labarai5 days agoHukumar Alhazan Jihar Jigawa ta Kaddamar da Kwamitin Amirul Hajjin Bana
-
Labarai2 days agoRadio Nigeria @75: Tsohon Dan Jarida Ya Yi Waiwaye Kan Tarihi Radio Nijeriya
-
Labarai7 days agoTrump Ya Aike da Daftarin Shirin Zaman Lafiya ga Iran
-
Labarai2 days agoMasarautar Saminaka ta Bukaci Hadin Kai Don Dorewar Zaman Lafiya a Yankin
-
Labarai2 days agoHukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Kammala Shirin Rigakafi ga Maniyyatan Bana
-
Labarai5 days agoHajjin2026: Jigawa ta Kara Kaimi Wajen Horar Da Maniyyata
-
Labarai2 days agoƊaya Daga Cikin Jariran nan Biyar Ya Rasu, Huɗu Na Ci Gaba Da Jinya a Asibitin Kano
